MATASHIYA: Wannan wani labari ne da PREMIUM TIMES HAUSA ta buga tun a ranar 13 Ga Yuli, inda aka yi nazarin kaka-gidan Boko Haram a jihohin Katsina da Zamfara. Mun sake kawo shi domin yi wa masu karatu matashiya kan yadda Boko Haram su ka samu gindin zama a yankunan, har su ka arce da daliban Kankara su 333 a Jihar Katsina.
Abubakar Shekau, gogarman ’yan ta’addar Boko Haram da aka rika yi wa kallon raini, ana ganin wa wani saida-kaji-saida-kaji, sai ga shi an yi sake ko sakaci, ya zama gawurtaccen gogarman da ke kokarin sayar da Arewacin Najeriya rankatakaf din ta.
Nazari ya tabbatar da wata shiryayyar ajandar da Shekau da mabiyan sa ‘yan Boko Haram ke kitsawa domin karasa mamaye Yankin Arewa maso Gabas, su darkake Arewa maso Yamma, kuma su dabaibaye Arewa ta Tsakiya.
Sabon Shirin Shekau Na Mamaye Arewa Kakaf:
A yanzu Shekau ya dawo ya na kulla kawancen sasantawa da juna tsakanin sa da wadanda ya rika kafirtawa da su ka balle, su ka raba hanya.
Sannan kuma ya rage zafi da radadin tsatstsauran ra’ayin saurin kafirtawa da ya ke yi. Ya kuma shata rawar da malaman cikin tafiyar za su rika takawa da matsayin zarata, dakaru da baraden-mutuwa-dole ke takawa a tawaga da rundunonin sa.
Ta kai a yanzu Shekau ya tashi tsaye ya na kokarin kafa kasaitacciyar daukar ‘Halifan Jihadin Afrika’ a karkashin ikon sa.
Ya yi yunkurowar da bai taba yin irin ta ba, tun bayan raba hanyar da ya yi da Al Qaeda cikin 2013.
Ba kamar yadda aka rika yi masa kallon wani galhanga ko wani garangaudiyar dan daba wanda da ke shirme a bidiyo ya na harba bindiga a sama a cikin bidiyo ko cika-baki ba, a yanzu Shekau ya zama wani gogan tsara dabarun yadda zai kai gaci ko tsallake siradi da tarko.
Masana tsiyar yakin sunkuru a Maiduguri da Abuja sun hakkake cewa ba a taba samun gogarman dan ta’addar da ya addabi wani yanki a cikin shekaru 10, har ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 30,000, sama da milyan 2 suka rasa gidajen su, kamar Shekau ba.
Tun bayan mutuwar Muhammad Yusuf cikin 2009, bayan Shekau ya hau ‘halifanci’, ya tsallake yunkurin juyin mulki da aka nemi yi masa ba sau daya ba – musamman har daga bangaren da ya fi shi kayan fama nesa ba kusa ba.
A yanzu Shekau ya zauna daram a kan kujerar sa, sai ma kokarin kara fadada ‘daular sa’ ya ke ta yi.
Sauya fasali da akalar jagorancin da Shekau ya yi, ta faro ne tun bayan zaman sa a Kano cikin 2012, zuwa hijirar da ya yi zuwa dajin Alagarno da Sambisa a Barno.
HumAngle ta gano cewa bayan Shekau ya rika shekar da jinainan daruruwan mabiyan sa saboda tankiyar da ba ta taka kara ta karya ba, sai gogarman ya gano cewa wannan danyen hukunci da ya ke yankewa ya janyo zaratan sa na ballewa daga gare shi su na arcewa cikin kasashen duniya. Har ma wasu na komawa bangaren Ansaru cikin 2012 da ISWAP cikin 2016.
Masu masaniyar lamurran da ke kai-kawo a Boko Haram, kamar yadda HumAngle ta ruwaito, sun nuna cewa sun fara fahimtar Shekau ya fara rage zafin akida, sai kuma sasautawa zafin da ya kan nuna kan kwamandojin sa. An hakkake a yanzu ya na ta kokarin sasantawa da mayakan sa da suka kauce daga wajen sa suka fandare masa.
“Sai dai kuma har yanzu an hakkake cewa ba ya ga-maciji shi da ISWAP.”
Gamin-gambizar Shekau Da ‘Yan-rugumutsi, Sa’alaba Da Bakura A Tabkin Chadi:
Yadda Shekau ke kara fadada yankunan da ke hannun sa a Yankin Tafkin Chadi, ya nuna irin hangen nesan da ya ke yi da muradin sa na kafa daular ‘halifanci’. Ga shi kuma har yau tabaran-hangen-nesan jami’an tsaro ya kasa hango tungar da Shekau ya yi tunga ko mashekari.
A Yankin Tafkin Chadi, Shekau ya kwantar da kai ya ja hatsabibin gogarma Sa’alaba da tantirin dan dadi-mutuwa, Bakura. Wadannan wasu rikakkun mayaka ne da suka ki mara wa kowane bangare baya, yayin da aka samu sabani tsakanin Abu Mus’ab dan Mohammed Yusuf da Mamman Nur, wanda rundunar sa ta ISWAP ta taba kece raini a da Boko Haram din Shekau cikin 2016.
Ganin yadda ‘yan ta’addar rundunar Sa’alaba/Bakura su sama da 300 suka hade a karkashin Shekau cikin Disamban 2018, ya sa a farkon 2019 ikon Yankin Tafkin Chadi mai arziki ya zama hannun bangarorin Shekau da na ISWAP.
Yadda Shekau ke kulla siyasar diflomasiyyar kulla yarjejeniyar zumunci tsakanin sa da kananan kungiyoyin ‘yan ta’addar da ke waje gefen Sambisa da Kudancin Barno wasu sassan Kamaru, ya na ba su iko/’yancin kai na su haren-haren daban, wannan na nuna irin mamayar da wannan kulla zumuci ya yi a kokarin da Shekau ke yi don zama Babban Kwamanda baki daya kuma ‘halifan daular’ da ya ke neman kafawa.
Tuni Shekau ke ta kokarin sake dinke baraka tsakanin sa da mayakan da suka balle, Amma kuma suka ki mika wuya ga tayin afuwar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi musu.
Wannan kuwa kamar wata karin magana ce da ake yi wa kazami, wai ‘dauda karin karfi wanda bai sani ba ka wanka.’
Hakan kuwa na kara wa Shekau karfi, kamar yadda wani tubabben dan Boko Haram ya bayyana wa HumAngle cewa bayan ya tsere daga Dajin Sambisa, cikin 2018, ta koma Kano, ya kasa samun aiki.
Irin haka ya sa masu wasu zaratan Boko Haram da dama sun kasa samun wurin zama a cikin al’ummar su a Arewacin Najeriya.
Kullum suna jin tsoron haduwa da wani dan Maiduguri da ya san su. Rayuwa ta zame musu jangwam.
“Wasu sun koma sun shiga Ansaru, sun darkaki Arewa maso Yamma, saboda sun kasa samun aiki ko madogara a cikin garuruwa.” Inji tsohon dan ta’addar.
“Amma yanzu tunda Shekau ya fadada ‘daular’ sa har Zamfara, ka ga kenan za mu iya komawa can mu mike kafar mu ba tare da tsoron komai ba.”
Majiya ta shaida wa HumAngle a ranar 16 Ga Yuni kamar yadda ta ruwaito cewa Shekau na ta kokarin kulla zumunta da mayaka a Taraba, Kogi, Katsina da Sokoto.
Sai dai ba a sani ba ko Gwamnatin Najeriya da sauran kasashen da ke yaki da Boko Haram na bibiyar wannan shiri da kulle-kullen fadada yankunan da Boko Haram ke ta kokarin yi.