Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa babu isassun cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da za su iya kula da mutanen kasar nan.
Ehinare ya ce gwamnati za ta kawao karshen wannan matsala nan ba da dadewa ba.
Ya ce barnatar da kudaden gwamnati musamman wadanda aka ware domin gina wurare kamar haka shine babban matsalar da ya gurgunta wannan fanni.
Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya a kasarnan sun bayyana cewa rashin inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na daga cikin dalilan dake kisan mata akalla kashi 80 bisa 100 a Najeriya.
Tolu Fakeye ya sanar da haka a taron kungiyar likitocin da suka kware a kimiyyar dakile yaduwar cututtuka na kasa (EPiSON) da ake yi a garin Jos, jihar Filato.
EPiPSON tare da hadin guiwar PACFaH@Scale ne suka shirya wannan taro domin tattauna irin gudunmawar da kungiyar za ta iya yi a wajen tsara hanyoyi da zai dakile ci gaba da yaduwar cututtuka a Najeriya da magance su.
Da yake jawabinsa Fakeye yace rashin samun shugabani na gari da wawushe kudaden da ake warewa cibiyoyin kiwon lafiya na daga cikin matsalolin da suka gurgunta harkar samar da kiwon lafiya a cibiyoyin tun bayan kafa su.
Ya kuma ce sauran matsalolin da ya mamaye cibiyoyin kiwon lafiya sun hada da rashin kwararrun ma’aikata, rashin ingantaccen wuraren aiki, rashin kayan aiki da sauran su.
Idan ba a manta ba shekaru hudu da suka wuce gwamnatin Buhari ta bayyana cewa za ta gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 10,000 a kasarnan.
Sai dai bayan wadannan shekaru cibiyoyin kiwon lafiyar na nan a cikin matsalolin da suke domin gwamnati bata tabuka abin a zo a gani ba tun bayan wancan furci da ta yi.
“A dalilin haka ya sa unguwar zoman gargajiya da magungunan gargajiya suke yin tasiri sannan manya manyan asibitocin dake kasar nan ke fama da yawan cinkoson mutane.
Bayan haka Fakeye ya ce domin samun mafita game da wannan matsala kamata ya yi ma’aikatan kiwon lafiya, malaman jami’o’I da duk sassan gwamnati su hada hannu domin farfado da wannan fanni.