” Ba zan bari wani ko wasu su kashe mana jam’iyyar da muke tunkagho da shi ba. Su za su iya komawa APC, amma ni ba zan iya komawa APC ba kuma ko da dama bazan koma ba. Saboda haka ina nan daram a PDP, babu inda zani sannan kuma na wasa wukake na domin guntule wa duk wani da ya ke neman ya kawo mana rudani a jam’iyyar.
Wadannan sune irin kalaman da gwamnan Jihar Ribas Nysome Wike ya yi a lokacin da yake hira da Talbijin din AIT ranar Juma’a.
” Ace wai muna jam’iyyar adawa, maimakon mu rika zama abar tsoro ga jam’iyya mai mulki sannan son kowa da kowa, amma mun zama fanko, ba mu iya komai saboda son rai. Kwamitin gudanarwar jam’iyyar ta zama sai yadda aka yi da ita, ta rube gaba daya. Maikamon yin abu don ‘yan jam’iyyar da mutane baki daya sun koma suna bin son zuciya. Su sani nan ba da dadewa ba asirinsu zai tonu.
” Ni dan jam’iyyar PDP ne amma kuma idan da za a tambayeni ko jam’iyyar za ta yi tasiri a 2023, zan ce a’a, domin komai na jam’iyyar a warwatse yake yanzu. Ya kamata ace mu yi amfani da gazawar APC a matsayin hanyar da za mu saida wa ‘yan Najeriya kan mu amma sai muka zamo muta ta watangaririya.
Discussion about this post