Ba za mu yi kasa-kasa ba wajen kawo karshen cin zarafin mata a jihar Bauchi – Gwamna Bala

0

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya yi alkawarin ci gaba da aiki da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a jihar domin kawo karshen cin zarafin mata ba.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamna Bala yayi a lokacin da uwargidansa Aisha Bala ta kai masa ziyara ofishinsa dake fadar gwamnatin jihar, a wani tattaki da kungiyoyin mata suka yi ranar Alhamis, ranar kyamatar cin zarafin mata.

Kamar yadda maitaimaka wa gwamna kan sabbin kafafen yada labarai Lawal Muazu ya fitar, gwamna Bala ya ce gwamnatinsa ta dauki kwararan matakai domin kawo karshen wannan mummunar abu, yana mai cewa mace daya da aka ci wa zarafi ya isa a dau mataki babba da zai kare sauran mata.

Sannan kuma ya ce tuni har gwamnatin sa ta umarci jami’an tsaro su maida hankali wajen bankado masu aikata haka sannan kuma da hukuntasu.

Kuma ya yi kira ga shugabannin addinai na jihar da masu ruwa da tsaki su rika ba jami’an tsaro hadin kai domin a samu nasara akai.

Daga farko dai uwargidan gwamna Bala, Hajiya Aisha Bala, ta bayyana cewa ta garzayo fadar gwamnati ne domin ta mika godiyar ta ga gwamna bisa goyan baya da yake bayarwa  tana mai rokon sa cewa kada ya karaya ya ci gaba da hakan.

Share.

game da Author