Ba za mu yarda a rika kiran Najeriya kasar da ta kusa durkushewa – Jam’iyyar APC

0

Jam’iyyar APC mai rike da akalar mulki, ta ki amincewa a kira Najeriya kasar da dab da rugujewa.

Masu sharhin al’amurran kasa da dama na fassara mummunar matsalar rashin tsaro da rugujewar tattalin arziki da kuma kuncin rayuwar da talata ke fama a kasar nan fiye da lokutan baya, cewa duk alamomi ne na kasar da kasa kai gaci, ta ke neman bingirewa.

APC ta ki yarda a kira bayyana Najeriya na neman ruftawa ramin da ba ta fiya fitar da kan ta. A kan haka sai APC ta ce “Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na iyakar kokarin ta wajen tabbatar da kawar da dukkan kalubalen da ke fuskantar kasar nan.”

APC ta ce yayin da masu yi wa kasar nan mummunar fata da ’yan-ba-ni-na-iya da ’yan adawa ke kauragiyar yi wa Najeriya mummunar fata, to su sani kasar mu kasaitacciya ce, kuma ba ta dauko hanyar durkushewa ba.

“Shugaba Muhammadu Buhari na sane da halin da kasar nan ke ciki, kuma ya na bakin kokarin sa, bai nuna gajiyawa ba, kuma bai yi wasarere da matsalolin da ke addabar kasar nan ba.

“Daga matsalar tattalin arziki zuwa matsalolin tsaro, abu ne mai sauki a rika cewa an dan fuskanci kalubale a kwanakin baya. Sai dai kuma gwamnati ta nuna namijin kokari cewa za ta iya dakile duk wata barazana ko kalubalen da ya tunkaro kasar nan, ko da na mahara da masu ta’adda da kuma na tattalin arzikin kasa.

APC ta yi maganar yadda gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen yi wa tsarin aikin dan sanda gwarambawul domin a samar da tsaro sosai a kasar nan.

Sannan kuma jam’iyyar ta buga misalai da tunatarwa dangane da yadda gwamnatin Buhari ta mike tsaye wajen hana kanana da manyan masana’antu da masu kananan sana’o’i durkushewa, sanadiyyar barkewar cutar korona.

“Maimakon APC ta biye wa shirmen PDP da ‘yan baranda ta rika caccakar sojojin Najeriya har ba su ganin kokarin da sojojin ke yi, to ita APC sai dai ta ci gaba da karfafa masu guiwa domin su dakile duk wata barazanar tsaro da ke tasowa a kasar nan.”

Share.

game da Author