Ba ni da matsala da gwamnati, ban saci ko sililin zare ba – Maina a kotu

0

Tsohon Shugaban Kwamitin Tsaftace Hukumar Fansho ta Kasa (PRTT), Andulrasheed Maina, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya cewa ba shi da wani markabun rikici tsakanin sa da Gwamnatin Tarayya, domin bai saci ko sililin zare ba.

A bayyanar da aka yi da shi a gaban Mai Shari’a Okon Abang a ranar Laraba, gungun lauyoyin Maina, ta bakin jagoran su, sun shaida wa kotu cewa ba su da wani sa-toka-sa-katsi tsakanin su da zarge-zargen da mai gabatar da kara daga bangaren EFCC, Ruqayyah Ibrahim ta zayyana wa kotu daya-bayan-daya.

Ruqayyah ta bayyana shigarwa da gabatar da bayanai dalla-dalla a gaban kotu, kafin a zo ranakun kira da gabatar da shaidu.

Bayan ta kammala, lauyan Maina ya fito a gaban mai shari’a ya na zaz-zaro mata tambayoyi. Inda bayan ta gama amsawa, ya ce shi ba-kare-damo tsakani Gwamnatin Tarayya da Maina, wanda ya ke karewa, domin bai saci ko sililin zare ba.

Bayan ya yi wannan furucin, Mai Shari’a Okon Abang ya aza ranar Juma’a, 10 Ga Disamba, domin lauyan na Maina ya fito shi ma ya yi wa kotu bayanai dalla-dalla wadanda zai kafa hujjar cewa ba-kare-bin-damo tsakanin EFCC da Maina.

A gabatarwar Ruqaiyyah lauyar EFCC, ta rika karanto yadda ta ce Maina rika lodi, jigila da saukalen makudan kudade daga banki zuwa wurin ‘yan canji da sunan bogi, inda ya rada wa kan sa suna Abubakar Mustapha.

Ruqayyah, wadda jami’ar EFCC ce mai bankado harkallar da aka taba ko da a cikin kogon dutse ce, ta shaida wa kotu yadda wasu mata uku Nafisatu Aliyu, Fatima Abdullahi da Fatima Aliyu su ka rika taya Maina lodi, jigila da saukalen kudaden.

Ana tuhumar Maina da caje-caje har 12. An gurfanar da shi bayan an kamo shi a jamhuriyar Nijar, a kokarin sa na arcewa daga Najeriya, bayan ya jefa Ali Ndume, Sanatan da ya tsaya masa beli cikin tsomomuwa.

Bayan dawo da shi Najeriya, Ndume ya shaida wa kotu cewa ya tsame hannun sa daga belin maina.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda aka damke Maina a Jamhuriyar Nijar, bayan ya jefa Sanata Ndume cikin tsomomuwar beli.

A yanzu dai Sanata Ali Ndume sai ya zuba ruwa kasa ya sha, domin jami’an EFCC tare da hadin kan jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar, sun yi cacukui ta Abdulrashid Maina, yayin da ya tsere cikin kasar.

Ya gudu ya tsere ne bayan da ya jefa Sanata Ali Ndume cikin tsomomuwar da ya kai Mai Shari’a Abubakar Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya, FCT Abuja ta tura shi kirkuku, bayan ya kasa kai Maina kotu, a karo uku bayan da ya karbi belin sa.

An tsare Ndume inda mai shari’a ya ce idan ba a samu Maina ba, to kotu za ta kwace naira bilyan 500 ta kudin belin da aka caji Ndume.

Sai dai kuma bayan Ndume ya shafe kwanaki biyar a tsare, alkali ya bada belin sa, bisa dalilin da’ar da kotu ta ce ya rika nunawa, inda bai taba fashin zuwa kotu ba, duk kuwa da cewa wanda ya karba belin ya tsere.

Maina, wanda shi ne tsohon Shugaban Kwamitin Sake Fasalin Fanshon Ma’aikatan Najeriya, ana zargin sa da kamfatar naira bilyan 2 tare da sayen manyan kadarori da kudaden.

Wannan daya ce daga cikin tuhume-tuhume 12 da ake yi masa, tare da wasu, ciki har da dan sa, wanda shi ma tuni ya cika wandon sa da iska, ya tsere bayan an karbi belin sa.

An samu nasarar kama Maina a Nijar, saboda kyakkaywar dangantaka tsakanin kasashen biyu, ciki har da yarjejeniyar hana wa gaggan masu wawurar dukiyar gwamnati mafaka a Nijar.

Share.

game da Author