Ba ni ba shugabancin APC kuma – Oshiomhole

0

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa babu shi babu sake shugabancin jam’iyyar, ko da kuwa Kwamitin Zartaswa na APC ya nemi sake damka masa rikon jam’iyyar a yau Talata.

“Ni fa yanzu an rufe shafin siyasa ta. Ko da kotu ta fito ta soke tsigewar da aka yi min, aka ce na dawo na ci gaba da shugabancin APC, to zan kare mutunci na, na ce ba zan karba ba, a nada wani.”

An dai rushe shugabannin APC a karkashin Oshiomhole watanni shida da su ka gabata, lokacin da wutar rikici ta tirnike APC.

Wannan ne ya sa aka nada shugabanni na riko, inda aka nada Gwamna Mala Buni na Yobe rikon jam’iyyar tsawon watanni shida.

Sai dai kuma maimakon a kira taron gangamin da za a yi zabe, sai Mala ya kira taron Kwamitin Zartaswa a yau Talata, wanda ake ganin dabara ce kawai ta kara wa kan su wa’adi.

Taron dai na daga gida ko ofis ne, wato ‘virtual’, kuma Shugaba Muhammadu Buhari zai halasta kai-tsaye daga ofis.

Bayan ya shafe watanni ba a ji duriyar sa ba, a wannan karo Oshiomhole ya fito ya na sukar masu zargin sa da cewa shi ne ke tunzira wasu mambobin Kwamitin Zartaswa na Oshiomhole da aka tsige, wadanda su ka garzaya kotu, duk kuwa da cewa Buhari ya ja kunnen yin haka din.

Oshiomhole ya ce shi babu ruwan sa, kuma tuni an tsige shi, har ya zama tarihi. Don haka babu hannun sa a batun shigar da karar da wasu su ka yi.

A karshe ya ce ya gode da irin goyon bayan da Shugaba Buhari ya rika ba shi.

Share.

game da Author