Ba mu yarda Buhari ya bayyana gaban ‘yan majalisa ba – Gwamnonin APC

0

Gwamnonin APC sun bayyana cewa basu amince shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gaban majalisar Kasa kamar yadda yayi alkawarin yin haka ranar Litinin.

Gwamnonin sun bayyana cewa yin haka zai iya ba ‘yan majalisar jihohi su rika yi wa gwamnonin irin wannan kiranye.

Gaba daya gwamnonin sun ce ba su yarda Buhari ya bayyana a gaban majalisa ba.

Sai dai kuma wasu daga cikin ‘yan majalisan da suka halarci wannan taro sun su hana shugaban kasa bayyana a gaban majalisa bai dace ba saboda ya riga ya amince kuma idan ya bayyana zai sama musu sauki bisa tsangwaman da suka sha a shiyoyyin su.

Gwamnoni sun ce sun bankado wani shiri da mambobin jam’iyyun adawa dake majalisar na sun kunyata shugaba Buhari idan ya bayyana a gaban su.

” Mun gano cewa mambobin jam’iyyar adawa sun shirya wani makircin su kunyata Buhari a majalisar idan ya bayyana. Idan muka bari hakan ya faru zai zama cin fuska ga jam’iyyar mu mai daraja, jam’iyyar APC da kuma shi kansa shugaban kasa.

Wani dan majalisa da ya halarci taron gwamnonin da jiga-jigan yan majalisar ya ce babu gaskiya cewa wai za a kunyata Buhari a majalisar.

” Mu ne muka fi yawa a majalisar, babu yadda za a ce wai muna gani za a kunyata shugaban mu. Amma kuma bayyanar sa gaban majalisa zai ba mutane daman sanin abinda Buharin yake yi kai tsaye. Sannan muma za mu samu sauki a shiyoyin mu.

Share.

game da Author