Kakakin majalisar Tarayya, Honarabul, Benjamin Kalu, daga jihar Abia kuma dan jam’iyyar APC ya karyata rahoton wasu kafafen yada labarai da suka ruwaito cewa wai ‘yan majalisar sun roki shugaban kasa yafiya a dalilin gayyatar sa majalisa.
Kalu ya ce ba majalisa bata roki Buhari yafiya ba, domin kuwa a cewar sa bata yi masa laifin komai ba.
” Aikin da mutane suka aiko mu mu yi muke gudanarwa a majalisa. Gayyatar da muka yi wa Buhari shima aikin mu ne, yaya za mu roki Buhari kuma don munyi aikin da ya kawo mu majalisa.
” Shi ma Buhari ya san abinda da dokar kasa ta ce, saboda haka ba zai kauce daga bin doka ba. Bai zo majalisar ba kuma ba mu roke shi yafiya ba.
Idan ba a manta ba, majalisar tarayya ta gayyaci shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a gabanta domin yi mata bayani game da rashin tsaro da ya yi tsanani a Najeriya.
Majalisar ta fusata ne bayan an yi wa wasu manoma kisan gilla a gonakin su a jihar Barno.
Wani dan majalisa daga jihar Barno, ya roki ‘yan uwansa su amince shugaban kasa ya bayyana a gaban su domin amsa tambayoyi.
Sai dai kuma duk da Buhari ya amsa kiran, gwamnonin jam’iyyar APC da ministan Shari’a sun hana shugaba Buhari bayyana a gaban majalisar.
Ita kanta jam’iyyar APC ta ce ta gono wani kulli na makirci da ake shirya wa Buhari idan ya bayyana a majalisar.