Jam’iyyar APC ta bayyana cewa ba ta za shiga zaben da INEC za ta gudanar ranar 9 Ga Disamba a Mazabar Bakura ta Jihar Zamfara ba.
INEC ta sanar da shirin ta na sake zaben ne a Mazabar Bakura, bayan ta bayyana zaben da ta gudanar a ranar 5 Ga Disamba cewa bai kammalu wa, wato ‘inkwankulusib’.
Shugaban Kwamitin Yada Labarai na APC ta jihar Zamfara, Ibrahim Magaji ne ya bayyana haka a taron da su ka yi da manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin dalilin da ya sa hukumar zabe ta bayyana rashin kammaluwan zaben a ranar 5 Ga Disamba, bayan ta soke zabe a rumfuna 14 na Karamar Hukumar Bakura.
INEC ta ce ta soke sakamakon zabukan rumfunan zaben ne, saboda yawan kuri’un da aka jefa sun haura yawan mutanen da su ka yi rajista a rumfunan zaben.
APC ta ce ta fasa shiga zaben, saboda babu sauran amana tsakanin ta da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma jami’an tsaro.
“Zaben da aka gudanar ranar Asabar ya dagule ta hanyar cin zarafin masu adawa da yi masu barazana, sai kuma yin awon gaba da malaman zabe da sauran nau’ukan rashin mutunci, ciki har da kisan jama’a.
“Wakilan APC sun je taron da INEC ta shirya a Gusau, a ranar 7 Ga Disamba, domin tattauna yadda za a gudanar da zabe lafiya. Taron ya kunshi dukkan wakilan hukumomin tsaro. Amma abin mamaki babu wani bangaren tsaron da ya halarci taron ko daya.
“Don haka mu na sanar da jama’a cewa APC ba za ta shiga zaben ‘inkonkulusib’, wanda za a gudanar a Bakura ba.