An yi wa manoma milyan biyar rajistar sayen taki cikin rahusa -Minista Nanono

0

Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta yi wa manoma milyan biyar rajistar samun tallafin takin zamani a cikin rahusa da rangwame.

Nanono ya bayyana haka a ranar Litinin, ya na mai cewa za su samu rahusar tallafin ne daga Shirin Wadata Manoma da Taki na Ofishin Shugaban Kasa, wato PFI.

A Abuja Nanono ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke ganawa da masu ruwa da tsari a harkar noma da takin zamani.

Cikin 2016 Gwamnatin Buhari ta kirkiro Shirin PFI domin kawadaitawa da tallafawa wajen samar da takin zamani a cikin kasa, da nufin a rage dogaro da shigo daga waje da ake yi.

Baya ga hada taki a cikin kasa, shirin PFI ya ta’allaka wajen ganin takin zamani ya karade yankunan kasar nan, ya wadaci manoma.

Masana’antun Harhada Takin Zamani a Najeriya dai a yanzu su na hada samfurin NPK har tan milyan hudu, sai kuma Urea tan milyan biyu a duk shekara.

Sannan kuma kididdigar gwamnati ta tabbatar da cewa masana’antun sarrafa takin zamani na da karfin daukar ma’aikata 250,000, wadanda ke amfana kai-tsaye da sauran wadanda ba kai-tsaye su ke amfana ba.

Yayin da ake kuka da tsadar taki, Nanono ya ce baya ga rajistar manoman da aka yi, kuma an yi rajistar gonakin su ta hanyar killace lambobin bayanan inda gonakin su ke a kwamfuta.

“Gwamnatin Tarayya ta fito da tsare-tsare masu yawan gaske domin tallafa wa manoma da marasa galihu, sakamakon matsin tattalin arzikin da annobar korona ta jefa milyoyin jama’a.

A kokarin da Gwamnatin Buhari ke yi domin rage dogaro da shigo da kaya daga waje, cikin watan Okton Nanono ya ce daga 2022 za a daina shigo da madara daga kasashen waje.

Nan da shekaru biyu masu zuwa Najeriya za ta haramta sha da shigo da madarar kasashen waje. Haka dai Ministan Ma’aikatar Gona, Sabo Nanono ya bayyana.

Ministan ya yi wannan jawabin a taron Tunawa da Ranar Abinci ta Duniya, a Abuja.

“Ku rubuta ku ajiye, nan da shekaru biyu za mu daina shigo da madara daga kasashen waje.

“Mu na da akalla shanu milyan 25 a kasar nan, sannan shanun nan da yawan masana’antun sarrafa madara sun kai akalla darajar naira tiriliyan 33. A kullum ana shan madara lita milyan biyar a Najeriya.”

Nanono ya ce nan ba da dadewa ba Najeriya za ta yi bankwana da yunwa da talauci ta hanyar bunkasa yalwar abinci da kiwo.

Ya ce a yanzu Najeriya ce ta daya wajen noma shinkafa mai tarin yawa, ba don komai ba, saboda an hana shigo da shinkafa daga waje, ana noma dukkan wadda ake amfani da ita a nan Najeriya. Wannan gwamnati ta bada himma wajen bunkasa noma, ta yadda kakaf yanzu a Afrika babu kamar Najeriya wajen noman shinkafa. Haka nan kuma Najeriya ce kasar da ta fi noma rogo a duniya, duk albarkacin himma da hobbasan da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi.”

Ya ce a yanzu haka Ma’aikatar Harkokin Noma ta tanadi kayan abinci mai tarin yawan metrik tan 109,567, kuma ana kyautata yakinin nan da karshen 2020 yawan abincin da ke ajiye a rumbunan Ma’aikatar Harkokin Noma zai rubanya zuwa tan 219,900.” Cewar Nanono.

Nanono ya yi dogon bayanin yadda wannan gwamnati ta samar da aikin yi ta fannonin noma daban-daban da kuma bunkasa abinci da fatattakar yunwa da kuncin fatara da talauci duk a lokaci guda.

Share.

game da Author