An tsiro da kamfen din goga wa Buhari kashin kaji – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta ce duk wani kulle-kulle da kicifin bata sunan Buhari da kokarin goga masa kashin kaji, ba za su yi tasiri a kan sa ba.

Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa “Gwamnatin Buhari ba za ta saki turbar da ta ke a kai ba ta yi wa jama’a aiki da gaskiya kuma tukuru, duk kuwa da rashin-ta-ido da shegantakun da wasu ke ta kitsawa don bata sunan Buhari a kasar nan.’’

Yayin da jama’a da dama ke ta korafi a kan matsalar tsaro a kasar nan, ita kuma Fadar Shugaban Kasa cewa ta yi wasu marasa kishi daga masu adawa da wadanda bas u kaunar gwamnati na ta kokarin daukar nauyin kamfen din bata wa Buhari suna, janyo masa bakin jini da kuma goga masa kashin kaji.

Adesina ya bayyana cewa kamfen din na bata sunan Buhari wasu marasa kishi ne za su fara dora shi a soshiyal midiya da nufin nuna wa duniya cewa wai ba shi ne rike da akalar mulkin Najeriya ba.

Ya ce tuni har wata jarida mai alaka da kasar waje ta fara kamfen din, ta hannun algunguman ta, masu zuga gwaiwa ta hau kaya.

“Ana ta kokarin watsa wa karnukan farautar su kudade a kafafen yada labarai na online. Wasu ma har sun karbi na su kason. Za su rika kirkiro labaraai na karya su na watsawa domin a shuka irin zaman gaba da kullatar juna a cikin kasa.

Adesina ya yi kira ga ‘yan Najeriya kada a dauke masu hankula daga soki-burutsun da wadannan marasa kishi za su bijiro ba shi.

Ya tuna wa ‘yan Najeriya alheran da ya ce ke cikin tafiyar gwamnatin Buhari, wadanda aka mora da kuma wadanda za a mora nan gaba,

Adesina ya sha su ka kwanaki uku da suka wuce, bayan da furta cewa ‘yan Najeriya su gode wa gwamnatin Buhari, domin duk da matsalar tsaro, yanzu bama-bamai sun daina tashi a kasar nan.

Share.

game da Author