A yanzu dai Sanata Ali Ndume sai ya zuba ruwa kasa ya sha, domin jami’an EFCC tare da hadin kan jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar, sun yi cacukui ta Abdulrashid Maina, yayin da ya tsere cikin kasar.
Ya gudu ya tsere ne bayan da ya jefa Sanata Ali Ndume cikin tsomomuwar da ya kai Mai Shari’a Abubakar Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya, FCT Abuja ta tura shi kirkuku, bayan ya kasa kai Maina kotu, a karo uku bayan da ya karbi belin sa.
An tsare Ndume inda mai shari’a ya ce idan ba a samu Maina ba, to kotu za ta kwace naira bilyan 500 ta kudin belin da aka caji Ndume.
Sai dai kuma bayan Ndume ya shafe kwanaki biyar a tsare, alkali ya bada belin sa, bisa dalilin da’ar da kotu ta ce ya rika nunawa, inda bai taba fashin zuwa kotu ba, duk kuwa da cewa wanda ya karba belin ya tsere.
Maina, wanda shi ne tsohon Shugaban Kwamitin Sake Fasalin Fanshon Ma’aikatan Najeriya, ana zargin sa da kamfatar naira bilyan 2 tare da sayen manyan kadarori da kudaden.
Wannan daya ce daga cikin tuhume-tuhume 12 da ake yi masa, tare da wasu, ciki har da dan sa, wanda shi ma tuni ya cika wandon sa da iska, ya tsere bayan an karbi belin sa.
An samu nasarar kama Maina a Nijar, saboda kyakkaywar dangantaka tsakanin kasashen biyu, ciki har da yarjejeniyar hana wa gaggan masu wawurar dukiyar gwamnati mafaka a Nijar.