Amurka ta bai wa sojojin ruwan Najeriya na’urorin inganta tsaron kasa

0

Amurka ta bai wa Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya makamai, a matsayin wani kokarin karfafa dangantaka tsakanin bangarorin tsaron kasashen biyu.

Tanko Fani, wanda ya wakilci Kwamandan Sojojin Ruwan Sashen Yamma Oladele Deji, ya shaida cewa kayan aikin da Amurka Ta bai wa sojojin ruwan na Najeriya, za su karfafa nagartar ayyukan da sojojin ruwan na Najeriya ke gudanarwa.

“A yau mu na kwarya-kwaryan bikin kayan fama na REMAC, kuma kayayyakin za su taimaka wasu kayan da aka bayar shekarun baya ga Rundunar Sojojin Saman Najeriya.

“Wadannan kayan za su warkar mana da ciwon matsalar da ke damun wannan bangaren, musamman kayan gyara da wadanda za a rika ajiyewa ko da wadanda ake amfani da su sun lalace, ai a sauya da su.

“Kuma muna jaddada cewa samun kayan RMAC zai kara karfin sa-ido da suntirin da sojojin ruwa ke yi da leken asirin samun bayanai na sirri.

“Wadannan kayayyakin su na rage mana asarar bata lokaci da wahalhalun zakulo bayanai. Domin amfani da kayan RMAC zai saukaka ayyukan sintiri.”

Ya ce Amurka na bai wa Najeriya goyon baya wajen bada horo ga sojojin wanzar da zaman lafiya.

Haka kuma Amurka ta na taimaka wa zaratan sojojin Najeriya wajen ba su kwararan horo na kwasa-kwasai na zahiri da kuma manyan makarantu da cibiyoyi.

Babban Jami’i a Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, Claire Pierangero, ta ce Amurka za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya wajen ganin an tabbatar da cewa tsaro a ruwan tekun Gulf of Guinea.

“Muna tabbatar maku da cewa mauyin da ya rataya a kan ku da kuma himma da jajircewar ku, ta zarce ta sauran kasashen da ke makwautaka da ku.” Inji Claire.

Share.

game da Author