Akalla mutum 12 suka rasu a hadarin mota da aka yi a hanyar Abuja-Kaduna ranar Laraba – Aruwan

0

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa akalla mutum 12 ne suka rasu a hadarin da wata babbar mota ta yi da wasu kananan motocin matafiya a titin Abuja-Kaduna.

Sannan kuma mutum 25 sun ji rauni a hadarin.

Aruwan ya ce hadarin yayi muni a dalilin suntuma gudu da miotoci ke yi da kuma bin hanyar da ba naka ba.

Wasu motoci sukan dauke hanya su bi hanyar da ba na su saboda su yi sauri.

Sanarwar da Aruwan ya fidda ta bayyana cewa tuni shi kansa da jami’an tsaro suka dira hanyar domin tilasta wa matafiya su bi hanyar su da ya dace. Idan kana zuwa ne ka bi, hanyarka, haka kuma idan kana dawowa ne shima ka bi hanyar ka.

Saboda tsananin lalacewar hanyar direbobi sukan canja hannun domin kauce wa fadawa rami a titin. Hakan na kawo yawan afkawa hadarin mota.

A karshe Kwamishina Aruwan ya gargadi direbobi da su rika kiyaye dokokin hanya yana mai cewa za a hukunta duk wanda aka kama yana karya dokar hanya.

Haka kuma shima gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya mika sakon jajen sa ga ‘yan uwan wadanda suka rasu a hadarin.

Share.

game da Author