Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga mata magoya bayan jam’iyyar PDP da Kwankwasiyya da su kimtsa majanyun su, tabarya da muciyar su su adana su a gefe, su saurari zaben 2023 a Kano.
Kwankwaso ya ce ba za su sa ido su bari wasu dake kan kujerun iko su yi musu dodorido a zaben 2023.
A jawabin da gogarman siyasan Kano, Kwankwaso yayi wa magoya bayan sa a Kano ranar Alhamis, ya ce, siyasar 2023, siyasa ce ta ko-anki ko-an-so.
Ya ce ba zasu yi hakuri su bari kirikiri a murde musu zabe da sunan ‘Inkonkulusib’ ba.
Ya ce idan ma suna da wata boyayyiyar shiri ne na hadin baki da hukumar zabe da jami’an tsaro, to wannan karon za a yi ta ta kare domin ba za su yarda.
Idan ba a manta ba, PDP ta yi laga-laga da APC a zaben Kano a 2019, inda bayan kirga kananan hukumomi 43 PDP ce ke kan gaba da sama da kuri’u 26,000, kafin aka bayyana ‘Inkonkulusib’.
Bayan sake zabe da aka yi a karamar hukumar Nasarawa, APC ce ta lashe zaben daga karshe.
Kwankwaso ya shaida wa magoya bayan sa a Kano cewa sun yi hakuri kuma suna nan suna jiran lokacin zabe.
” Sun dauka 2023 ba za ta zo ba, muna nan dai ga shi a kwana a tashi yanzu sai gangara ya rage.