2023: Jonathan ya ki nesanta kan sa da sake tsayawa takaran shugaban kasa

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonarhan, ya ki nesanta kan sa daga tunanin sake tsayawa takarar shuganan kasa a zaben 2023.

Lamarin ya faru a wani taro, yayin da manema labarai su ka yi masa tambaya kan zargin ana zawarcin sa, domin ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

A wurin taron Jonathan ya amsa wa manema labarai cewa, “a yanzu dai lokacin da mutum zai yi magana kan siyasa ko makomar siyasar sa, bai yi ba tukunna.”

Kwanan nan ana rade-radin cewa jam’iyyar APC na zawarcin Jonathan domin ya amince ta tsayar da shi takara, saboda ana ganin idan ya amince, zai iya rufa wa shugabannin da ke kan mulki a yanzu asiri idan sun sauka.

Sannan kuma dangane da hayagagar maida mulki kudu, idan Jonathan ya yi nasara, to zango daya na shekara hudu kadai zai yi, tunda ya taba yin zango daya daga 2011 zuwa 2015.

An fara gasgata wannan rade-radi ganin yadda Shugaban Riko na Jam’iyyar APC, kuma Gwamnan Yobe, Mala Buni, ya ja gayyar zugar gwamnonin APC, su ka je har gidan Jonathan a Abuja, su ka yi masa gaisuwar murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Ziyarar kuwa ta yi daidai da lokacin da gwamna Dave Umahi ya fice daga PDP ya koma APC.

Jonathan dai ya sha kaye a kokarin sa na yin tazarce a hannun Buhari a zaben 2015.

Da ya ke magana a kan rashin tsaro, Jonathan ya roki jama’a su goya wa gwamnatin Buhari baya, domin ta samu ta yi nasara kan ta’addanci da hare-haren garkuwa da mutane.

Ya ce ba Najeriya kadai ce kasar da ke fama da matsalar tsaro ba.

Tun bayan da Jonathan ya sauka, ya bada karfi wajen gaganiyar sasantawa bangarori da kawo zaman lafiya a kasashen Afrika, sai kuma aikin sa-ido a kan zabuka a Afrika.

Share.

game da Author