Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Frank Mba ya bayyana cewa rundunar ta dawo da Abdulrasheed Maina gida Najeriya, bayan an bankado in da yake boye a kasar Nijar.
” Ina mai sanar muku cewa rundunar ƴan sandan Najeriya sun dawo da Abdulrasheed Maina wanda ya aka gano inda ya ke boye a kasar Nijar.
Kwamishinan ƴan sanda Garba Umar ne ya jagoranci jami’ai zuwa yaso keyar Maina daga Nijar zuwa Najeriya.
Akarshe ya ce za a mika Maina a kotu kamar yadda ta umarta domin a cigaba da shari’ar zargin handame kudaden ƴan fansho da yayi a lokacin da yake shugabantar hukumar.
Maina, wanda shi ne tsohon Shugaban Kwamitin Sake Fasalin Fanshon Ma’aikatan Najeriya, ana zargin sa da kamfatar naira bilyan 2 tare da sayen manyan kadarori da kudaden.
Wannan daya ce daga cikin tuhume-tuhume 12 da ake yi masa, tare da wasu, ciki har da dan sa, wanda shi ma tuni ya cika wandon sa da iska, ya tsere bayan an karbi belin sa.
An samu nasarar kama Maina a Nijar, saboda kyakkaywar dangantaka tsakanin kasashen biyu, ciki har da yarjejeniyar hana wa gaggan masu wawurar dukiyar gwamnati mafaka a Nijar.
Shi dai Maina ya gudu ya tsere ne bayan da ya jefa Sanata Ali Ndume cikin tsomomuwar da ya kai Mai Shari’a Abubakar Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya, FCT Abuja ta tura shi kirkuku, bayan ya kasa kai Maina kotu, a karo uku bayan da ya karbi belin sa.
An tsare Ndume inda mai shari’a ya ce idan ba a samu Maina ba, to kotu za ta kwace naira bilyan 500 ta kudin belin da aka caji Ndume.