Iyayen daliban da aka sace a Ƙanƙara sun yi tir da gwamnatin APC, ƙarkashin shugaba Muhammadu Buhari da gwamna Aminu Masari kan rashin iya ceto ƴaƴansu da masu garkuwa suka yi garkuwa da su a makaranta.
” Da na san ire-iren abubuwan da za mu afka ciki kenan a kasar nan, da ban wahalar da kaina na fita zabe ba. Tsakani na da wannan gwamnati, sai muce Allah ya saka mana, amma sun watsa mana kasa a Ido, ace yara sama da 300 a tafi da su har yanzu shiru.
” Da ni da makwabtana, ƴaƴan mu takwas suke tsare a hannu masu garkuwa da mutane. Yaya za muyu da ran mu tsakani da Allah. Idan an kashe su ne, a kawo mana gawarwakin su nu binne abin mu, amma tsakani da Allah shiru kwanaki sai tafiya suke kuma wai ace akwai gwamnati a kasa.” Binta Ketare-Maiwaina
Ita Hajiya Fa’iza, cewa ta yi ta na Abuja aka kira aka wai fa danta dake makarantan na daga cikin wadanda aka sace.
Iyayen dai gaba dayan su cikin jimami kira suke yi ga gwamnatin Najeriya, ta gaggauta dawo musu da ‘ya’yan su.
” Yau da ace ƴaƴan su ne za ke manyan makarantu, da tuna an san inda aka dosa, kuma an ceto daga maharan.
Yadda maharan suka afkawa makarantar Kankara
” Ina tsaye bakin get din shiga makaranta muna sauraren dalibai su gama karatun ‘Prep’ na dare mu kashe wutan makaranta kowa ya je ya kwanta kwatsam sai muka ji harbin bindiga ta ko-ina babu kakkautawa.
” Juyawan da zan yi sai naga ɗan sandan da ke tsaye kusa da ni ya fadi kasa, sun harbeshi a wuya. Sadab-sadab sai na boye wajen Asambili. In kallon su.
” Sun dan dauki lokaci suna bata kashi da jami’an tsaro da na sa-kai kafin nan wasun su suka kutsa cikin makarantar suka tattara ɗaliban.
” Sai da ya dauke su awa 5 suna kwashe daliban, domin sun iso makarantar da misalin Karfe 10 na dare ne ba su tafi ba sai waje karfe biyun dare.