Gwamna Babagana Zulum na Barno ya bayyana cewa sai an hada da tasirin siyasar karfafa al’umma idan ana so a magance Boko Haram.
Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, ranar da ya gana da Shugaba Buhari, inda ya yi masa karin haske dangane da ci gaban da aka samu a matakan tsaro a Barno.
Ya bayyana abin da ke faruwa a Barno da “tantagaryar hauka.”
Zulum wanda ya bayyana haka a ganawar da ya yi da Shugaba Buhari a ranar Juma’a, ya ce karfin soja kadai ba zai iya magance bala’in Boko Haram ba.
Ya bayyana yadda gwamnnatin sa ta maida ‘yan gudun hijira 100,000 daga sansanoni zuwa gidajen su.
Zulum ya ce domin a dakile Boko Haram, tilas sai an tallafa kuma an bunkasa rayuwar matasan jihar, domin su samu hawa turbar rayuwar neman abin dogaro da kai a cikin ingantacciyar al’umma.
” Ina farincikin shaida wa Najeriya cewa ana ci gaba da samun zaman lafiya a Arewa maso Gabas, musamman a jihar Barno.” Inji Zulum.
“Gwamnati ta fara kwashe jama’a daga sansanonin masu gudun hijira zuwa gidajen su.
“Mun samu gagarimar gudummawa daga sojoji da sauran bangarorin tsaro, Ma’aikatar Kudade, Ma’aikatar Harkokin Agaji da Jinkai da Inganta Rayuwa, NEMA da Hukumar Farfado da Yankin Arewa ta Gabas.
“Yadda ake kwashe masu gudun hijira zuwa garuruwan su, wata alamar fara wanzuwar zaman lafiya ce a jihar Barno.
“Mu na bukatar ci gaba da samun cikakken goyon baya daga sojoji. Kuma mu na bukatar taimaka wa matasan mu domin su samu dogaro da kai, a daina wannan hauka a ake yi, mu kawo kawo karshen sa.”
“Da farko na a ce akwai bukatar magance asalin abin da ya fara haddasa wannan bala’i a Barno. Wannan kuwa kuwa ba wani abu ba ne sai fatara da yunwa.
“Tilas sai gwamnatin tarayya, ta jiha da ta kananan hukumomi su sa himma wajen samar wa matasa sana’o’in dogaro da kai a cikin al’umma.
“Ina ganin wannan shi ne hanya mai iya kawo karshen karshen ta’addacin da ake yi a Barno. Domin a gaskiya karfin soja kadai ba zai iya murkushe Boko Haram ba.”
Da ya ke magana a kan zanga-zangar #EndSARS kuwa, Zukum ya jinjina wa matasan Barno da su ka ki shiga. Ya na mai cewa zanga-zanga ita ce tushen ba’ilin da har yau ya ke addabar jihar Barno.