Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta jihar Bauchi (BSPHCDA) ta bayyana cewa cutar shawara ta barke a karamar Hukumar Ganjuwa.
Hukumar ta ce mutum takwas sun mutu sannan sakamakon gwajin da aka gudanar ya tabbatar cewa cutar shawara ce tayi sanadiyyar rasuwar su.
Shugaban Hukumar Rilwanu Mohammed ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Litini a garin Bauchi.
Rilwanu ya ce Hukumar ta samu labarin barkewar cutar ne daga wajen masu yawon yi wa yara allurar rigakafin cutar shan inna.
” Sun iske mutum 8 sun mutu a dalilin kamuwa da wata cuta da ba a san irinta ba.
” An debi jinin wadannan mutane domin yi musu gwajin cutar zazzabin lassa da shawara inda sakamakon ya nuna cewa cutar shawara ce suke dauke da shi.
Rilwanu ya ce hukumar za ta fara yi wa mutanen karamar Hukumar allurar rigakafi domin dakile yaduwar cutar.
” A Bara war haka cutar ta bayyana a kananan hukumomi shida da suka hada da Bauchi, Alkaleri, Warji, Ningi, Kirfi da Darazo.
Ya kuma shawarci mutane da su rika amfani da gidan sauro domin kare kai daga cizon sauro da kamuwa da zazzabi.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar Zazzabin shawara
1. A yawaita amfani da gidan sauro idan za a kwanta.
2. Tsaftace muhalli musamman nome ciyawa a harabar gida da rufe ruwan da ake tarawa domin hana sauro.
3. A saka raga a taguna da kofofin gida domin hana sauro shigowa gida.
4. A fesa maganin sauro domin kashe sauro da kwari.
5. A tabbatar an yi wa yara allurar rigakafin cutar sannan manya za su iya zuwa asibitin gwamnati domin yin allurar rigakafin cutar kyauta idan ba su yi ba.
6. Ma’aikatan kiwon lafiya su zage damtse wajen yi wa duk mara lafiya gwajin cutar.
7. Ya Zama dole ma’aikacin kiwon lafiya ya Kare kansa yayin da yake kula da Madi fama da cutar.
Discussion about this post