ZARGIN HARKALLA: Fowler, Tsohon Shugaban Hukumar Tara Haraji (FIRS) ya bayyana ofishin EFCC

0

Tsohon Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida, Babatunde Fowler, ya bayyana ofishin Hukumar EFCC a ranar Litinin.

Kakakin Yada Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa gayyatar sa aka yi ofishin, kuma ya kai kan sa a ofishin EFCC na shiyyar Lagos a ranar Litinin.

Sai dai EFCC ta bayyana dalilan gayyatar sa din ba.

Fowler kafin shugabancin FIRS daga 2015 zuwa 2019, ya yi shugabancin Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Lagos, tsawon shekaru takwas. Shi ne ma shugaban ta na farko.

Buhari ya tura masa takardar gargadin sanin dalilin da ya sa FIRS ya kasa tara haraji mai tsawon shekara hudu, ganin cewa tun 2015 a lokacin Jonathan ba a kara tara mai yawa a wata shekara ba kamar na 2015.

Cikin Disamba, 2019 Buhari ya cire shi, ta hanyar kin kara masa wa’adi karo na biyu, bayan ya kammala zangon shekaru hudu na farko.

An maye gurbin sa da Mohammed Nami, wani kwararren masanin hanyoyi da yadda ake tatsar haraji iri daban-daban a hannun jama’a, masana’antu, kamfanoni da ‘yan kasuwa.

Tun bayan hawan Nami gwamnatin Buhari ke kirkiro haraji daban-daban.

An kara harajin-jiki-magayi, an dawo da harajin-ladar-ganin-ido da kuma harajin-la’ada-ciki, wato na ‘stamp duty’, wanda ko hayar gida za ka bayar, sai ka ciri la’ada ka bai wa Gwamnatin Tarayya.

Share.

game da Author