Shugaban kasar Amurka Domald Trump ya bayyana cewa bai yarda da sakamakon zaben da aka sanar ba wanda ya nuna ya saha kasa a zaben.
Trump ya ce idan dai shine to kowa ma ya koma ya daura damarar fafatawa da shi domin yanzu aka fara domin bai amince da sakamakon zaben ba.
Joe Biden na jam’iyyar Democrat ya lashe kuri’un jihohin da ake bukata dan takara ya lashe zaben shugaban kasa a Amurka.
Sai dai Trump ya ce an yi masa murdiya a zaben.
Tuni dai har tsohon shugaban Kasa, Barak Obama ya mika wa zababben shugaban kasa Joe Sakon murnar yin nasara a zaben.
A Najeriya ma, Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Joe Biden sakon taya murnan lashe zaben.
” Daga ranar litini, lauyoyin mu za su fara shigar kara kotunan zabe domin a bi mana hakkin mu a maida min da kujerata ta shugaban kasa da aka yi min karfa-karfa a kai.
” Mutanen Amurka na son a yi zabe ne mai nagarta wato sahihin zabe wanda za a kirga kuri’un gaskiya, ba kuri’un karya ba wanda basu ba. Saboda haka ba zan taba yin hakuri sai an baiwa ‘yan Amurka abinda suka zaba ba wanda aka zabar musu ba.
Discussion about this post