ZABEN AMURKA: Ko an sake Kirge a Georgia, nasara na tare da mu – Inji Biden na Democrat

0

Ɗan takaran shugaban kasar Amurka na jam’iyyar Democrat, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana wa magoya bayan sa cewa su kwantar da hankalin su, nasara na tare da su a wannan zabe.

Biden ya fad haka ne a jawabin da yayi wa magoya bayan sa a cikin daren Juma’a.

Biden ya ce shi fa har ya shirya tsaf don fara aiki gadan-gadan domin ga dukkan alamu ya riga yayi nasara a zaben.

Akwai sauran wuraren da ba a kammala kirga kuri’un su ba, daga wadanda aka kirga ma zuwa yanzu a wadannan wurare ma kawai mune a kan gaba.

Sai dai kuma shugaban kasar, Donald Trump ya ce kame-kame kawai Biden yake yi domin shine zai lashe zaben Amurka din.

Democrat sun yi mana murdiya a wasu jihohin da muke da tabbacin cewa mune zamu yi nasara a amma kuma cikin dan kankanin lokaci sai suka murde zaben, suka canja alkaluma zaben.

” Muna nan muna bibiyar komai daki-daki, dalla-dalla kuma da idanun mu kuru-kuru a bude, yanzu dai za a sake kirge a Georgia, sannan lauyoyin mu a shirye suke domin kalubalantar zaben a babbar Kotun Amurka da zarar an bayyana wani ba mu ba shugaban kasa.

Har yanzu ba a kaiga karkare kirgan kuri’un ƴan Amurka a wasu jihohin kasar da haka yasa ba za a iya cewa Biden na Democrat ya lashe zaben kai tsaye ba.

Share.

game da Author