ZABEN AMURKA: Ana shirya yi min murdiya a zabe, A dakatar da kirge – Trump

0

Shugaban Kasar Amurka, kuma dan takarar Republican, Donald Trump ya zargi masu kirgen kuri’un zaben da su dakata a wasu jihohin kasar yana mai cewa ana kokarin yi masa murdiya.

Wankin hula dai na neman ya kai Trump Dare a wannan zabe, ganin cewa Joe Biden na Democrat sai wawushe kuri’un sauran jihohin da suka rage yake yi a baya-bayan nan.

Shugaban Kasar Amurka, kuma dan takarar Republican, Donald Trump ya ce an ya ko ba ayi masa murdiya a wasu wuraren bai sani ba.

Trump ya ce, a baya nine ke kan gaba a iya kuri’un da aka kirga har da wadanda suka fito daga jihohin da Democtrat ne ke da karfi a can wuraren.

Sai gashi yanzu kwatsam alkaluman sai canja wa suke yi, Democrat ce ke ta yin sama, sama, wato dan takara Joe Biden.

Duk da dai cewa har yanzu ana kan-kan-kan ne duka ƴan takaran na ganin shine zai yi nasara a zaben, wanda ake sa ran kammalaci ranar 10 ga Nuwamba.

Kusan duk awa sai shugaba Trump ya rubuta abinda ake ciki a zaben.

A jiya da safe ya mika gidiyarsa ga mabiya wata Coci a Najeriya, da suka bi tituna suna tika rawa suna mai waka don ya samu nasara a zaben.

Shi ko Biden na Democrat, ya jaddada wa magoya bayan sa cewa nasara na tare da su a wannan zaben.

Ba sai za a san maci tuwo ba sai miya ya kare.

Share.

game da Author