Za mu murkushe duk wanda ya sake bijiro wa da Zanga-zangar #EndSARS – Rundunar ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Legar ta gargadi masu shirin bijiro da sabuwar Zanga-zangar #EndSARS a jihar Legas da su shiga taitayin su, cewa wannan karon, ba za su ji da dadi ba.

” Bayan jin jiki da mutanen legas suka yi da asarar dukiyo da har yarzu ba’a farfado ba, ‘rundunar ‘yan sanda da wasu hukumomin tsaro sun gano wata shiri a boyi da ake yi na sake kaddamar da sabuwar zanga-zangar a jihar a karo na biyu.

” Mun samu wadannan baya nai na sirri, kuma masu shirya zanga-zangar na so su bijiro da ita ne don wani nufi na su. Amma kuma su zani ba za mu nade hannu mu zuba musu ido ba. Wanda aka yi a baya har yanzu ko kusa da farfadowa daga hasarar da aka yi ba a yi ba. ” Inji kakain ‘Yan sandan Legas.

A karshe rundunar ‘Yan sandan ta gargadi wadanda ke shirin shirya wannan Zanga-zanga su sake tunani. Sannan kuma ta yi kira ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yan su kada su kuskura su biye wa masu shirya wannan zanga-zanga.

Legas na daga cikin jihohin basu sha da dadi ba a lokacin wannan zanga-zanga, domin baya ga asarar da mutane suka yi na dukiyoyi da rayuka hatta jami’an tsaro dake aiki a jihar sun tsira ne da kyar, wasu ma sun rasa rayukan su baya ga ragargaza ofisoshin su da matasan suka yi.

Share.

game da Author