Za a gina cibiyar koya wa masu digiri da difiloma sabbin dabarun fiɗar shanu, tumaki da awaki

0

Gwamnatin Jihar Lagos ta bayyana cewa za ta mayanka da mahauta ta zamani, inda za ta koya wa rundawa dabarun fidar dabbobi ta zamani.

Gwamnatin jihar ta ce za a gina cibiyar domin ta rika bada horo ga sabbin-shiga harkar pawa da tsoffin rundawa dabarun yanka dabbobi, fidar su da tsaftace naman kamar yadda kasashen da su ka ci gaba a duniya ke yi.

Kwanishinan Harkokin Gona na Jihar Lagos, Abisola Olusanya ne ys bayyana haka, a lokacin da ake gwajin shirin fara aiki a karamar mayankar shanu da awaki ta hadin guiwa tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa, a Bariga, Lagos.

Harkar pawa ta kunshi yanka dabbobi da fedewa ana sayar wa dillalan nama danyen nama a Lagos.

Olusanya ya ce za a gina cibiyar ce domin karfafa wa wadanda su ka kammala digiri da sauran matasan jihar guiwa kutsa kai cikin harkar pawar danyen nama a mayanka, har su samu tsayuwa da kafafun su a hada-hadar.

“Za mu karkato hankalin matasan da su ka kammala digiri, difiloma da sauran natsatstsun game-garin matasa yadda ake cin moriyar sana’ar danyen nama a zamanance.” Inji kwamishina.

“Ba za mu iya jawo hankalin su a sana’ar danyen nama ta gargajiya da ake yi a kwatar mayanka ba, saboda babu tsafta.”

Kwamishinan ya ce wannan cibiyar da za a kafa za ta zama ta farko irin ta a Najeriya.

Ya nuna damuwa kan yadda ake yawan samun haramtattun mayanka a Lagos, wadanda ya ce kafa cibiyar zai shafe su kakaf.

Share.

game da Author