Za a cika wa Najeriya aljifai da dala milyan 300, fam milyan 60, wadanda Abacha da Ibori su ka boye a Ingila da Ireland

0

Mataimakin Daraktan Kungiyar Adalci ga Muhalli da Tattalin Arzikin Afrika (ANEEJ), Leo Atakpu, ya bayyana cewa kwanan nan Ingila za ta dumbuza wa Najeriya fam milyan 60, wadanda tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ya ce ya boye a London.

Ibori wanda ya yi gwamnan Delta, jiha mai arzikin man fetur daga 1999 zuwa 2007, ya yi zaman kurkuku a Ingila, bayan kotun kasar ta kama shi da laifin harkalla da jigilar kudaden Haram a cikin kasar daga Najeriya.

Tuni dai ya kammala wa’adin sa har ya dawo Najeriya, bayan Birtaniya ta kwace kudaden a hannun sa.

Atakpu ya ce akwai kuma zunzurutun dala milyan 300 da kasar Ireland za ta maido wa Najeriya kwanan nan, daga kudaden da tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha ya sata, ya boye a can kasar.

Ya yi wannan bayani ne a wani taron kungiyar sa ta shirya a Benin, babban birnin jihar Edo.

Ya ce Ingila na nan na tattaunawa da Najeriya inda ta ce za ta bayar da kudaden da Ibori ya sata, amma ta na so ta sa-ido ta tabbatar cewa an yi wa talakawa ayyukan da za su ji a jikin su cewa gwamnati ta tuna da su.

Kudaden da Abacha ya sata da za a maido har dala milyan 300 kuwa, wannan ne karo na hudu da za a maido wa Najeriya makudan kudaden da Abacha ya sata.

Su kuma wadannan kudade har dala milyan 300, an kulla yarjejeniya da Ireland cewa za a kashe kudaden wajen aikin Gadar Kogin Neja da ake kan ginawa a yanzu, sai aikin fadada titin Lagos zuwa Ibadan da kuma aikin titin Abuja zuwa Kaduna.

Akwai kuma dala 900,000 da aka kama a hannun tsohon gwamnan Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha, wadanda Atakpu ya ce an amince za a gina cibiyoyin kula da lafiya da kudaden idan an maido wa Najeriya su.

An kuma amince za a baiwa Jihar Delta kashi 30 visa 100 na kudaden da Ibori ya sata idan an maido su Najeriya kwanan nan.

Share.

game da Author