Yunƙurin neman ƙara zuba jarin naira bilyan 3.3 ya haifar ruɗani a Bankin Jaiz

0

Yunƙurin neman kara zuba jarin naira bilyan 3.3 ya haifar da ruɗani a Bankin Musulunci na Jaiz Bank.

Hukumar Gudanarwar Jaiz Bank da kuma masu hannayen jari a ciki, sun sanar cewa Bankin Jaiz ya fara kokarin samun ganin cewa ya kara tara yawan jari na naira bilyan 3.3, ta hanyar yi wa jama’a tayin hannayen jari har 5,076,923,077 da ta kama daga kwabo 50k zuwa kwabo 65.

Sai dai kuma tun daga ranar da mahukuntan bankin su ka yi wannan sanarwa, har yau sun kasa fara aiwatarwa.

Hakan kuwa ya samo asali ne daga wata tankiya da sabani a kan shekarun ka’idar aiki da Manajan Darakan Jaiz Bank da kuma sabo nada wanda ya gaje shi.

Sai dai kuma bankin ya musanta cewa rashin wai sabanin ya haifar da babbar baraka a bankin.

Da ya ke warware yadda lamarin ya ke, Bankin Jaiz ya bayyana cewa babu wata rashin jituwa ko sabani kamar yadda ake tunani.

Cikin jawabin wanda aka fitar ranar Lahadi a Abuja, Jaiz ya bayyana cewa, “Mu na yin kira da jan hankali ga hukumomin kula da bankuna, masu zuba jari, sauran bankuna, masu hannayen jari da sauran jama’a cewa babu wani sabani ko rashin jituwa a cikin mambobin gudanarwar Jaiz kan ayyukan da su ka jibinci daraktocin wannan bankin.”‘Inji Jaiz.

Domin bankin ya nuna babu wani cikici tare da shi, a ranar 28 Ga Oktoba, 2020 ya sanar da neman masu bukatar zuba jari su sayi hannayen jarin bankin.

An fito da wannan sanarwa ce bayan tashi daga taron hukumar daraktocin Jaiz karkashin Shhgaban su, Umar Mutallib.

Jaiz ya ce an yanke shawarar neman kara jarin bankin ne saboda amincewa da yardar da masu ruwa da tsaki na bankin ya yi wa bankin, duk kuwa da kalubalen da aka fuskanta a lokacin zaman korona a jida.

Batun rashin jituwa kuwa a kan nada sabon wanda zai gaji na yanzu da ke kai, ya ce mahukuntan bankin sun amince da haka, domin wa’adin wanda ke kai ya kusa kammala wa’adin sa.”

“Yayin da wasu ke ganin cewa idan wanda ke kan shugabanici ya sauka, to ana wani da zai kawo canjin kara bunkasa da ci gaban Jaiz.

“Wasu kuma na ganin tunda dai wanda ke kan shugabancin ya kawo canje-canje masu ma’ana, kuma ya bunkasa bankin, to a iya kara masa wa’adin ci gaba da rike bankin.”

Duk da haka, sai bankin ya zarce ya nada Muhammad Shaheed Khan, a matsayin sabon Manajan Darakta wanda zai gaji mai barin gado kwanan nan.

Nada Khan da aka yi ya haifar da rudani a Jaiz Bank, har ma ta kai su ga warware nadin a taron su na biyu bayan nadin.

Kafin ya tabbata sabon Manajan Darkata dai sai Babban Bankin Najeriya CBN ya amince da nadin tukunna.

Tun kafin CBN ya amince ko ya ki amincewa, sai aka warware nadin da aka yi wa sabon manajan daraktan.

Jaiz ya tabbatar wa kwastomomi da masu zuba jari cewa komai na nan daram a bankin babu wani rudu.

Share.

game da Author