‘Yan sandan Kano sun cafke Uba, Uwa da Da da ke harkallar saida ganyen Wiwi a Kano

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ta damke wani matashi mai suna Kabiru Mahmud da lodin kullin ganyen wiwi har 49.

Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa ya shaida haka da yake tabbatar da cafke Kabiru a zantawa da yayi da PREMIUM TIMES ranar Laraba.

Kiyawa ya ce Kabiru mazaunin Danbire ne kuma an kama shi a lokacin da ya fito daga gida da wiwin wai zai kai ajiya wani gida a bayan layin su.

Kiyawa ya kara da cewa wasu mutanen kirki ne suka garzayo ofishin ‘Yan sanda suka kawo karan harkallar da Kabiru da mahaifinsa suke yi.

Da ake tuhumar sa a caji ofis, Kabiru yace shima ya gaji saida ganyen wiwin ne daga mahaifin sa wanda ya yi shekara sama da ashirin yana sana’ar saida ganyen wiwi.

Ya ce a wajen sana’ar saida da wiwi ne jami’an tsaro suka Kama Shi.

Kabiru ya kara da cewa bayan mahaifin an kama mahaifinsa, shine mahaifiyar sa ta tace lallai ya zo ya kwashe sauren wiwin dake ajiye a gida gudun kada jami’an tsaro su sake garzayowa bincike gan su, ya ja musu tashin hankali.

A yanzu dai Kabiru, mahaifinsa da mahaifiyar su na tsare a ofishin ‘yan sanda.

A karshe rundunar ‘Yan sandan sun ce za su mika su duka ga sashen da ke hukunta masu laifi irin haka na jihar.

Share.

game da Author