‘Yan sanda sun fara yi wa jiga-jigan #EndSARS tsintar-farin-balbela

0

Kwanaki kadan bayan da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bai wa Babban Bankin CBN umarnin kulle asusun ajiyar kudaden wasu jiga-jigan zanga-zangar #EndSARS su 20, ‘yan sandan Najeriya sun fara farautar wasu su na damkewa.

Jami’an ‘Yan Sandan Binciken Manyan Laifuka na FCID sun dira gidan mawaki kuma dan gaba-dai-gaba-dai din zanga-zangar #EndSARS a Lagos, Eromosele Adene, su ka karya kofar da karfin tsiya su ka yi gaba da shi.

An kama Eromelese ranar Asabar, daga bisani kuma aka dauko shi cancak daga Lagos zuwa Hedikwatar FCID da ke Abuja.

An kama shi ne bayan ya fara raba fasta-fastar kyallen yadi mai dauke da bayanin a fito a sake wata sabuwar zanga-zanga.

An rika nuno wani faifan bidiyo a shafin sa na Twitter, inda ake ganin gungun ‘yan sanda sun isa kofar gidan sa a mota, su na kokarin karya kofar su shiga.

A shafin na Twitter din, Eromelese ya yi bayanin cewa, “Gwamnati ta turo a kama ni, saboda kawai na bayyana ‘yancin ra’ayi na. Yanzu haka ga ‘yan sanda nan sun karya kofar gidan. To ga su nan ma sun shigo.”

Sun Tsare Shi Kwana Uku Ba Su Kai Shi Kotu Ba -Lauya

Lauyan sa mai suna Obona, wanda shi ma dan rajin kare hakkin jama’a ne, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ci gaba da tsare Eromesele karya doka ce kuma haramci ne.

Ya ce ko kafin a baro Lagos da shi ya sha wahala a can.

Kama shi ya biyo kama su masu zanga-zanga shida a Abuja da ke tsare a Suleja.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Fadar Shugaban Kasa ta sha alwashin duk wadanda su ka kitsa zanga-zangar #EndSARS, sai sun dandana kudar su.

Share.

game da Author