Mahara ɗauke da bindigogi sun dira kauyen Yolde Pate dake karamar hukumar Yola ta Kudu inda suka yi garkuwa da wata mata da yaron wani dan sanda.
Maharan sun hada da wani dan bijilante a kauyen amma ya arce da raunin harsashi a jikinsa da kyar.
Mazauna da jami’an tsaron dake kauyen sun ce maharan sun shigo kauyen a daren Litinin. Maharan sun dauki tsawon minti 30 a kauyen ba tare da wani jami’in tsaro ya kawo musu taimako ba.
“Maharan sun far wa gidan jami’in tsaron dake kusa da Kurkukun Yolde Pate da misalin karfe 11:50 na dare.
” Ƴan sanda sun zo kauyen bayan maharan sun yi awon gaba da matan da yaron wanda mahaifinsa jami’in tsaro ne dake aiki a Abuja.
Kakakin rundunar’yan sandan jihar Suleiman Nguroje ya tabbatar da haka yana mai cewa kwamishinan Ƴan sanda ya bada umurnin a ceto mata da yaron da suka arce da su daji.
Nguroje ya yi kira ga mutane da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kama mahara a jihar.
“Wannan shine karo na biyar da mahara fe afka wa wannan kauye a jere a jere.