Yadda mahara suka daka warwason masallata a masallacin Juma’a a Zamfara

0

Wani abin tashin hankali da ya auku a karamar hukumar Maru, jihar Zamfara ya bar mutane cikin juyayi da ɗimuwa.

Wannan abin tashin hankali ya da ban tsoro kuwa shine yadda wasu mahara suka diranwa masallacin Juma’a, a daidai masallata sun cika fam liman har ya iso, suka tarwatsa su.

Wani mazaunin garin da abin ya faru a idon sa ya shaida cewa maharan sun afka musu a daidai suna shirin tada sallar Juma’a.

” A daidai muna kokarin tada sallar Juma’a sai maharan suka afka mana. Daganan fa sai kowa ya zuba da gudu. Wasu da yawa sun tsira amma harsahi ya cimmusu, sun samu rauni a jika.

” Maharan sun daka wa masallata warwaso inda suka tafi da mutum 40. Sun yi wannan abu cikin kwanciyar hankali domin ko wulkawar jami’an tsaro bamu gani ba.

Majiyar mu ta ce, maharan sun bi ta kauyuka daya bayan daya a hanyarsu suna kashe na kashewa sannan suna kwashe duk wani abin amfani da suka cimma kafin suka iso masallacin.

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar abinda ya faru sai dai ta ce mutum 18 ne mahara suka arce da su sannan suk kashe wasu mutum biyar.

Hare-haren da garkuwa da mutane ya kazanta a yankin Arewa Maso Yamma, inda ya kazanta a jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna.

Share.

game da Author