Wani hoto da Rahama Ta saka a shafinta ta Tiwita da Instagram ya jawo cece-kuce har da zage-zagen addini a tsakanin masoyanta da masu binta a shafukan yanar gizon.
Rahama ta saka wasu hotunanta a shafukanta inda ta caba kwalliya da wasu irin kaya wanda kusan rabin bayan ta a waje yake ta bankare domin hoto yayi kyau.
Bayan su ta dauki wasu wanda ba su nuna haka ba.
Sai dai saka wadannan hotuna ke da wuya sai shafukan ta ana yanar gizo suka kama da wuta. Wasu na cewa tir da saka wannan hoto wasu kuma suma hoto yayi kyau.
Cece-kucen bai tsaya a nan ba, domin har ya kai ana sukan addabi ni a ciki ana zage-zage da ya izgilanci a tsakanin masu yin sharhi.
Daga baya dai Rahama ta cire wadannan hotuna sannan ta saka wasikar nuna rashin jin dadinta ga wadanda suka wuce gona da iri, suka afka hurumin da ba nasu, wato hurumin addini, sannan tace duk abinda ya hada yi wa addininta izgilance ba za ta bari ba.
Ta ce ba za ta yi shiru ba ta bari a maida shafinta da hoto da ta saka wajen sukar addininta ba, ta ce addininta da annabinta SAW ba abin wasa bane.
Rahama ta ce ba ta saka hotunan don ta bata wa wasu rai ko kuma ta tada hankalin jama’a ba sannan ta ce ga wadanda abin ya bata wa rai su yi hakuri.