Yadda Allah ya kubutar da ni daga gaggan ‘yan fashi a hanyar Abuja – Basaraken Adavi

0

Sarkin Adavi dake jihar Kogi Muhammad Ireyi Bello ya bayyana yadda ya kubuta daga shiga hannun ‘yan fashi da makami a hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Bello ya ce sun gamu da ‘yan fashin ne a kauyen Magajiya da kan titin Abuja-Lokoja.

Ya ce ya je Abuja ne domin halartar addu’o’in rasuwar wani jami’in hukumar RMAFC Suleiman Kokori da ya rasu.

Wani dan uwan basaraken da suke tare, Bello Otaru Abduljafar ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da aukuwar haka ranar Juma’a.

Bello ya ce ‘yan fashin sun afka musu a daidai sun isa wannan gari mai suna Magajiya, dama kuma wannan wuri bashi da kyau, titin ya lalace sosai, dole matafiyi ya je a hankali, daga nan ne sai ‘yan fashin suka diran musu.

Cikin ikon Allah sai direban ya samu ya waske da gudun tsiya a daidai su kuma maharan sun ta harbi da bindiga, kuma babu wanda ya ji ciwo a cikin motar.

Basaraken yayi kira ga rundunar tsaron kasa da su saka jami’an tsaro a wannan hanya domin rashin su ne ke sa mahara na samun daman afkawa matafiya a duk lokacin da suka iso musamman wannan wuri da titin yayi mummunar baci.

Wannan titi shima ya na daga cikin titunan da suka yi kaurin suna wajen fashi da makami da ake yi wa matafiya a yankin Arewa.

Share.

game da Author