Yadda ƴan iska su ka yi kisan-gilla, kone dukiyoyin a dalilin zanga-zangar #ENDSARS a Abuja

0

Attahiru Muhammad ya fita ya bar gidan sa a kauyen Apo, can gefen Abuja kusa da kasuwar saida kayan gyaran motoci da ake kira Apo Mechanic Village. Ya fita da niyyar komawa gida, amma ashe tafiya ce ba ta komawa gida ba.

Matasa ƴan iska, ƴan buyagi da ƴan sara-suka, sun cimma Malam Attahiru daidai lokacin da ya ke gaggawar zuwa ganin yadda aka banka wa masallacin sa wuta.

Ba masallacin sa kadai aka banka wa wuta ba. An banka wuta a wasu shagunan kasuwar, sannan aka kone motoci 11 a garejin Patrick Okara.

Tunda farko, wadannan ƴan iska wadanda kai da gani ka san ba zaunannun cikin garin Abuja ba ne, sun tarwatsa masu zanga-zangar #ENDSARS a Asokoro da randabawul din hanya mai zuwa Apo daga Abuja. Sun rika bin su da sara, jifa, duka da kone-kone.

A wannan rana ce ta 20 Ga Oktoba su ka ragargaje Apo, inda cikin wadanda aka kashe, PREMIUM TIMES ta tabbatar akwai Attahiru Muhammadu, dattijo mai shekaru 80 a duniya.

Attahiru: Ya Gudu Bai Tsira Ba

A takaice Attahiru da matar sa Adama da sauran ƴaƴa bakwai, duk zaman gudun-hijira su ke yi a kauyen Abuja. Daga jihar Zamfara masu garkuwa su ka fatattake su.

Masu tarzomar fasa taron #EndSARS sun cim masa, aka falla masa sara da adda ko takobi har aka kusa fille masa kai.

Wasu da dama na zargin cewa jami’an gwamnati ne su ka dauko ƴan iskan domin su fasa taron #EndSARS.

An kafta wa Haruna sara a hannu a lokacin da aka ritsa su za su dauki gawar Muhammadu.

“Kai na su ka so faskarewa da adda, amma sai na tarbe da hannu na. Shi ne aka ji min rauni a hannun.”

Patrick Okara na cikin aiki a garejin sa, sai ya ga dafifin ƴan takife da makamai sun tunkaro shi gadan-gadan.

“Ai da na sheka a guje ban san lokacin da na haye kan tsauni ba. Ban sauko ba sai cikin dare.”

Motoci 11 masu tarzoma su ka banka wa wuta a garejin Patrick.

Baya ga asarar rayukan da aka yi, babu wanda aka yi wa mummunar barna kamar John Ositachukwu. An kona bargar motocin da ke ofishin sa kakaf. Cikin su har da samfurin BMW E65, wadda ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ita kadai kudin ta ya kai naira milyan 160.

“Ina aiki cikin ofis sai aka kira ni a waya, aka sanar da ni masu tarzoma sun banka wa masallacin kasuwa wuta har da shagunan kusa da masallacin.

“Sai na ci gaba da aiki, a rai na na ce, ai ni ba dan zanga-zanga ba ne.

“Bayan kamar minti uku sai na ga cincirindon jama’a dauke da muggan makamai sun taso min gadan-gadan.

“Tun da na ke a duniya ban taba yin irin gudun da na yi a ranar ba. Su ka fasa ofis aka kwashe komfutoci da kaya aka kuma lalata shi.

“Kiyasin asarar motocin da na yi sun kai na adadin naira milyan 300.” Inji OsitaChukwu.

Yayin da Adama matar marigayi Attahiru ke neman a bi hakkin mijin ta, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Ministan Abuja da ya kai ziyarar ganin barnar da aka yi, iyakar sa bakin masallacin da aka kona, bai karasa gidan mamacin ba. Sannan kuma bai karasa garejin Okara da ofishin Ositachukwu ba. Ballantana a tantance diyyar da gwamnati ta sha alwashin biya ba.

PREMIUM TIMES ta kasa samun karin haske daga kakakin Ministsn Abuja ba. Kuma ba ta samu bayani mai gamsarwa daga kakakin ‘yan sandan FCT Abuja, Mariam Yusuf.

Share.

game da Author