WHO ta yi kira da a maida hankali wajen dakile yaduwar cutar dajin dake kama mahaifar mace a duniya

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta tsara wasu hanyoyi da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar dajin dake kama mahaifar mace a duniya.

Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya ce wadannan hanyoyi sun hada da inganta yin gwaji, bada maganin cutar da yi wa mata rigakafin cutar.

Ghebreyesus ya ce amfani da wadannan matakai za su taimaka wajen rage kashi 40 bisa 100 na matan da ke kamuwa da cutar da rage akalla mata miliyan 5 da cutar ke kashewa daga nan zuwa 2050.

Cutar dajin dake Kama mahaifar

Dajin dake Kama mahaifar mace cuta ce da za a iya warkewa idan an gano cutar da wuri sannan an juri shan magani.

An fi kamuwa da wannan cuta ne idan mace na yawan saduwa da maza ba tare da tana amfani da kwaroron roba ba.

Kasashen duniya sun yi nasarar dakile yaduwar cutar amma bullowar cutar korona ya dawo da hannu agogo baya.

Binciken da WHO ta gudanar a shekaran 2018 ya nuna cewa a duk shekara mata 14,943 ne ke kamuwa da cutar inda daga ciki 10,403 na mutuwa.

WHO ta yi kira ga kasashen duniya da su karfafa gwaji, bada magani da yin rigakafin cutar domin dakile yaduwar cutar.

Burin kawar da cutar

Burin WHO shine kawar da yaduwar wannan cuta gaba daya daga duniya daga nan zuwa shekaran 2030.

Hakan zai hada da yi wa mata kashi 90 bisa 100 masu shekara 15 allurar rigakafin cutar, yi wa kashi 70 bisa 100 na mata masu shekaru 35 zuwa 45 gwajin cutar.

Sannan da tabbatar cewa kashi 90 bisa 100 na matan da suke fama da cutar sun samu magani.

WHO ta ce Idan ba a gaggauta dakile yaduwar cutar ba a duniya, za a samu karin yawan wadanda za su kamu da cutar daga 570,000 zuwa 700,000 sanan cutar za yi ajalin mata 311,000 zuwa 400,000 daga yanzu zuwa 2030.

Share.

game da Author