Watanni uku bayan hadimin Ganduje ya damfari malamai kuɗaɗen addu’ar korona, har yau Ganduje bai ce komai ba

0

Watanni uku kenan bayan hukumar dakile zamba ta Jihar Kano ta kama Mashawarcin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da laifin damfarar malamai kudaden ladar yi wa cutar korona addu’o’i, har yau gwamnan bai dauki matakin hukunta ba.

Bayan kama Ali Baba, hukumar ta kuma kwato kudaden daga hannun sa, sannan ta maida wa malaman da ya damfara hakkin su.

An zargi Ali Baba da laifin damfarar daruruwan malaman da Ganduje ya tattara a ranar 30 Ga Yuli, domin yin addu’ar Allah ya raba Kano da cutar korona.

An dai tara malamai sama da 300, wadanda bayan kammala addu’a aka ba Ali Baba kudaden sallamar su, amma ya zabtare kudaden ya yi masu wawakeken gibi.

Bayan kammala taro, Kwamishinan Harkokin Addinin Musulunci, Muhammad Tahir ya shaida wa malaman a cikin Dakin Taro na Africa House da ke cikin Gidan Gwamnatin Kano cewa akwai sallama za a ba kowa naira 50,000.

Amma maimakon mai sallamar su, Ali Baba ya ba kowanen su naira 50,000, sai ya ba kowa naira 5,000, ya soke naira 45,000 din kowane malami a na sa aljihun.

Shugaban Hukumar Hana Rashawa na Kano, Muhyi Magaji, ya tabbatar da kwato kudaden a hannun Ali Baba, kuma aka bai wa kowane malamin hakkin sa.

Sai dai ya ce sun maida hankali ne wajen kwato kudaden kawai, ba tare da hukunta Ali Baba ba, saboda an yi taron addu’o’i ne saboda Allah.

Shi ma Kwamishinan Yada Labarai na Kano Muhammad Garba, ya ce gwamnati ba ta shiga lamarin ba, saboda ba za ta shiga aikin hukumar hana cin rashawa ta Kano ba.

Shi kuwa wanda ya damfari malamai milyoyin kudaden, cewa ya yi ba satar kudaden ya yi ba. Ya ce ya rage wa kowa nasa kason ne, domin ya kara tattara sunayen dimbin malamai masu yawan gaske, ya tsits-tsinka wa kowa na sa hasafin.

Share.

game da Author