TSADAR FETUR: Motocin Buhari, Ministoci da tirelolin Dangote sun koma amfani da gas – Ministan Fetur

0

Karamin Minstan Man Fetur Timiprey Sylva, ya bayyana cewa tsadar fetur ya sa an maida dukkan motocin ofishin sa amfani da gas, kuma ana kan maida na Ofishin Shugaba Muhammadu Buhari, na Ministoci da na Majalisar Dattawa da ta Tarayya zuwa amfani da gas.

Da ya ke tattaunawa sa PREMIUM TIMES a ofishin sa, Minista Sylva ya ce tuni manyan tirelolin kamfanin Dangote ma duk sun koma amfani sa gas.

“Kuma an shaida min a yanzu haka kamfanin na Dangote na samun saukin kashe kudaden shan mai da kashi 50 bisa 100. Wato a yanzu rabin abin da ake kashe wa motocin ga fetur ne ke isa a sayi gas.

Minista ya ce wannan ce mafitar samun sauki, kuma nan da ranar 30 Ga Nuwamba, 2020 za a kaddamar da shirin a kasa baki daya.

Wannan bayani ya zo daidai lokacin da farashin mai ya tashi daga naira 161 ya koma naira 170.

Ƴan Najeriya na ta tofin Allah wadai da karin fetur din da za a fara dandanawa daidai karshen shekara.

Da ya ke magana, Sylva ya ce an zo lokacin da za a daina dogaro da fetur a matsayin abin zuba wa mota, saboda tsadar sa.

Ya kuma yi kukan cewa duk da Najeriya na sahun farko na kasashe masu arzikin gas a Afrika, ya ce har yanzu ba a amfani da gas sosai a Najeriya, sai dai a birane da manyan garuruwa kadai.

“Mun kammala tattaunawa da Ministoci dangane da maida motocin su masu amfani da gas. Su ma Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya, za mu zauna da su, domin tattauna batun maida na su motocin gaba daya masu amfani da gas, domin ya fi sauki sosai. Inji Sylva.

Share.

game da Author