TARIN FUKA: Hada hannu da mazauna gari zai taimaka wajen hana yaduwar cututtuka a kasar nan – Kwararru

0

Wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun yi kira ga gwamnati ta rika saka mazauna gari a duk lokacin da take yin wani tsari na inganta kiwon lafiya a kasar nan.

Kwararrun sun ce yin haka zai taikama wajen dakile yaduwar cututtuka a Najeriya.

Wadannan kiraye-kiraye da sauransun ya biyo bayan zaman wani taro ne da kungiyoyi masu zaman kansu ‘Civil Society Accountability Forum’ da ‘Stop TB Partnership Nigeria’ suka yi domin samun madafa wajen kawar da cututtukan zazzabin cizon sauro, tarin fuka, kanjamau da korona.

Shugaban kungiyar ‘Stop TB Partnership Nigeria’ Ayodele Awe ya ce idan a aka rika yin haka, ana yin tafiya da mazauna wuraren da ake aiki, za a samu nasara matuka wajen kauda rashin sani a tsakanin mutane da kuma wayar musu da kai game da matakan da za su rika bi don kauce wa kamuwa da cututtuka da kuma yada su.

Awe ya ce wani binciken da aka yi a 2012 ya nuna cewa kashi 75 na mutanen dake fama da tarin fuka mazauna kauyuka ne.

Ya ce a dalilin haka yake da mahimmanci gwamnati ta hada hannu da mazauna gari domin samun nasara musamman wajen yaki da cututtuka da yaduwar su.

Tarin fuka: Shan magani da yin allurar rigakafin cutar na daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cutar.

Najeriya na daya daga cikin kasashe 30 da wannan cuta ta yi wa katutu a duniya kuma itace kasa ta farko da cutar ta fi yawa a Nahiyar Afrika.

A 2019 kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta lissafo kasashe takwas da suka fi fama da cutar a duniya.

Wadannan kasashe sun hada da India, Chana, Indonesia, Philippines, Pakistan, Najeriya, Bangladesh da Africa ta Kudu inda daga ciki India, Chana da Najeriya ne kasashen da suka fi yawan mutanen dake fama da cutar.

Sakamakon binciken da UN ta gudanar ya nuna cewa a duk shekara mutane 245,000 na rasa rayukansu a dalilin kamuwa da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author