Asusun bada Tallafi na duniya wato Global fund, ya bayyana cewa a cikin shekaru uku Asusun zai tallafa wa Najeriya da dala miliyan 143 domin yaki da tarin fuka.
Jami’in yaki da cututtuka na asusun Eliud Wanerdwalo ya sanar da haka a taron da kungiyar ‘Stop TB Partnership’ ta shirya a makon jiya a Abuja.
Wanerdwalo ya ce asusun zai baiwa wa Najeriya zunzurutun kudi har dala miliyan 500 tare da wasu kasashen Afrika 10 domin yaki da tarin fuka a cikin shekara uku masu zuwa.
Kasar Kongo, Ethiopia, Ghana, Kenya, Mozambique, Afrika ta Kudu, Tanzania, Uganda, Kamaru da Zambia ne kasashen da za su ci moriyar wannan tallafi.
Wanerdwalo ya ce asusun zai kashe dala biliyan 12.7 a kasashe masu tasowa domin yaki da cututtukan kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro.
A dalilin annobar korona akwai yiwuwar samun karuwar akalla mutum miliyan 6.3 da za su kamu da cutar, mutum miliyan 1.4 da za su mutu a dalilin tarin fuka a duniya daga wannan shekaran 2020 zuwa 2025.
Gano mutanen dake dauke da cutar
Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya koka kan yadda gano masu fama da cutar ko yi wa gwamnati wuya domin a basu magani da ake bayar wa kyauta.
Ya ce dole a maida hankali wajen yin binciken wadanda ke fama da cutar musamman mata da yara kanana sannan kuma a tsananta yin gwaji domin rage yaɗuwar cutar.
Shugaban mataimakin kungiyar ‘Stop TB Partnership’ Suvanand Sahu ya ce taron Wanda ya gayyaci ministocin kiwon lafiya da wasu jami’an gwamnati na kasashen Afrika 11 ya tattauna hanyoyin dakile yaduwar tarin fuka musamman a wannan lokaci da duniya ke fama da annobar korona.
Discussion about this post