Talakawa suna cikin mawuyacin hali a Najeriya, Daga Bashir Dambam

0

Idan za’ayi magana ta gaskiya a cire son kai da akidar siyasa tare da kawar da makauniyar soyayyar da mukeyiwa shugabannin mu tun daga kan shugaban kasa har izuwa chairman na kananan hukumomi banajin acikinsu kashi dari (100%) akwai kashi talatin (30%) wanda adalcinsu ga al’ummar da suke mulka zaisa su koma kan kujerunsu.

Amma saboda mafi yawa daga cikin al’ummar kasar mu basusan minene mulkin dimokaradiya ba muna ganin kamar mun waye a siyasa amma har yanzu bamu waye da ita ba,

Dalili kuwa shine:

Idan kaji mutum yana cewa wani mutum yana da adalci to tabbas yana bashi na cefa ne ne, shi ba damuwarsa wannan mutumin yayiwa al’ummar daya ke mulka wani abinda zasu mora ba a.a shi indai za’a masa to kowa ma ya rasa, Kuma zakaga ta ko yaya yana naiman kalaman da zaiyi amfani dasu wajen tabbatar wa duniya cewa wai gwaninsa mai adalci ne koda kuwa yasan hakan karyane.

Babu wani dan siyasa da komai kankantar kujerarsa da bazai iya kawo wani abin cigaba wa al’ummarsa ba, Ni a ganina kawo wa ci gaba a al’umma ba akan kujerar da kake zaune yake ba a zuciyarka yake koda kuwa kai kansila ne akwai abin cigaba da zaka iya kawowa a al’ummarka…

Amma bayan duk wannan babu wanda talaka yafi tsammanin samun sauyi daga wurinsa a yanzu cikin ikon ubangiji sama da shugaba Muhammadu Buhari, Talakawan kasata NIGERIYA sunyi amfani da duk wani abu nasu wajen ganin samun nasarar shugaba Buhari akan samun Mulkin shugabancin NIGERIA, Talakawa sunyi amfani da dukiyoyinsu da kudinsu da Iliminsu da Basirarsu da lokacinsu domin samun nasarar shugaba Buhari sun
hana idanuwnasu bacci ba dare ba rana sunyi addu’a cikin ikon Allah aka samu nasara, ba wani abu bane yasa sukayi wannan sadaukar war sai don Kyakkyawan zato da tsammani da sukeyi akanka cewa kaine zaka iya kawo musu dauki akan irin hali na matsi da kuncin rayuwa da suka samu kansu aciki.

Idan talaka yace yana neman canji ba kudi yake bukata ka bashi ba a’a saukin rayuwa yake nema ta dalilinka.

Shugaba Buhari Talakawa sun zabeka saboda suna tsammanin samun sauyi ta bangarori Kamar:

1- Samun tsaro a kasa: ta hanyar kare musu lafiyarsu da dukiyoyinsu

2- Samun saukin rayuwa: ta hanyar rage kudin kayan masarufi da rage kudin man fetur

3: Bangaren Noma: Bada tallafi a manoma domin inganta gonakensu

4: Raya Birni da Karkara: Ta hanyar samar da wutar lantarki

5: Samar da aikinyi: Samarwa matasa aikinyi ta hanyar basu aiki da bude masana’antu daban daban aduk fadin kasarnan

6: Inganta Bangaren Ilimi: Ta hanyar inganta makarantu tare da rage kudin makaranta da kuma bada tallafi a dalibai wato Scholarship.

Tambaya a gareku Shugabannin mu ?

Shin
Tun daga kan Shugaba Buhari da duk wani mutum mai mulki a kasarnan ta wani bangare ne daga cikin abinda na lissafa talaka ya samu sauki ta dalilin Mulkinku

Shin
Wannan shine Chanjin ?
Wannan Shine Cigaban

Banda yan tsirari masu kokari acikinku irin su zulum.

Wasu sun rasa rayukansu ta dalilin zabanku, wasu sun rasa dukiyoyinsu wasu sun rasa gidajensu amma sbd rashin sanin dalilin dayasa talakawa suka zabeku hakan be dameku ba.

Kuna kwana cikin AC cikin daula bakwa ziyartar mazabanku taya zaku gane irin halin da talkawa suke ciki a kasarnan.

Muddin talakawa bamu daina yin makauniyar soyayya a shugabanni ba mun daina kwadayi mun fuskanci gsky da gsky ba to wlh haka zamuyi ta kukan zcy har iya tsawon rayuwarmu…

Mu daina tunanin sanja shugabanni duk bayan shekara hudu wai chanji ne, wlh haka zasuyi ta xuwa a iya mulkin shekara hudun da sukeyi suna iya satar kudin da zai ishesu iya tsawon rayuwarsu basuyi talauci ba.

Mu talakawa mune zamu fara kawo chanji ta hanyar zaban shugabanni na gari ba tare da sonkai ko akidar siyasa ba..

Allah yasa duk mu gane, Allah kuma ya kawo mana chanji

Daga
Comr Bashir Suleiman Bash Dambam

Share.

game da Author