Majalisar Sojin ta amince da karin girma ga wasu sojoji zuwa mukamin Manjo Janar, Birgediya Janar, Kanal da Laftanar Kanal.
Karin mukamin ya kunshi Birgediya janar 39 wadanda aka kara musu girma zuwa mukamin Manjo Janar da masu mukamin kanal 97 zuwa matsayin birgediya janar.
An kara wa Laftanar Kanal 105 mukami zuwa Kanal, sannan kuma masu mukamin Manjo 180 an kara musu girma zuwa mukamin Laftanar Kanal.