Sufeto janar din ƴan sandan Najeriya ya umarci kwamishinan ƴan sandan Najeriya na Kaduna da ya binciki badakalar hoton jaruma Rahama Sadau da ya jawo cece-kuce a shafukan yanar gizo a kasar nan.
Idan ba a manta ba tun bayan saka wani hoto da jaruma Rahama Sadau tayi wanda a dalilin hoton wani mai binta a shafin ta na yanar gizo ya yi izgilanci ga Annabin tsira, SAW, mutane suka rika fitowa suna tsina ne mata albarka.
Rahama ta fito daga baya ta roki ƴan Najeriya amma kuma da yawa daga cikin mutane musamman abokan aikinta a Kannywood sun ci gaba da nuna rashin jin dadin su akai ta hanyar fitowa suna ci gaba da caccakar ta.
Kamar yadda jaridar Fim Magazine ta buga, wani Mal Mohammed Gusau ne ya kai karar Rahama ga Sufeto Janar din Ƴan sanda inda ya nemi hukuma ta yi maza-maza ta saka baki a cikin wannan magana tunda wuri.
A dalilin haka har wasu daga cikin jaruman baya wato Hafsat Shehu da Mansurah Isah suka rika cacan baki da tone-tonen asiri a tsakanin duka a dalilin kare jarumar.
An dai ce Rahama da mahaifiyarta, da ƴan uwanta duk sun dira Abuja domin waskewa zuwa Dubai kafin sakon Sufeto Adamu ya iske ta.