Rundunar Sojojin Najeriya ta kaddamar da gagarimar rundunar hadin-guiwa tsakanin sojoji da ‘yan bijilante na CJTF domin farautar wasu rikakkun ƴan Boko Haram 84.
Abubakar Shekau, Albarnawy da Ibrahim Abu Maryam na cikin wadanda ake nema ruwa jallo.
Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ne ya kaddamar da farautar tare da Gwamna Babagana Zulum, a Hedikwatar CJTF, wato ‘Super Camp’ da ke Chabal, kusa da Maiduguri.
Wannan ne karo na hudu, kuma rukuni na hudu ana fito da sunayen ‘yan Boko Haram da ake farauta.
Wasu daga cikin wadanda ke jerin sunayen dai tun cikin 2016 aka fara buga sanarwar neman su. Wasu kuma sabbin zubin sunaye ne, daga baya kurar su ta yi kuka, har aka fara farautar su.
A yayin kaddamarwar, Buratai ya bayyana cewa wasu da ake farautar su tun 2016 sunayen su na cikin wadannan sunaye 84.
“Amma wasu da ake nema tun 2016 din kuma, an kashe su wurin arangama, wasu kuma sun tsere, sun boye, an daina jin duriyar su.
Daga nan sai Buratai ya yi kira ga daukacin jama’a da CJTF su bada hadin kai wajen wannan gagarimin aikin.
Ya ce wajibin jama’a ne su rika bada rahoton wadanda ake cigiya din da kuma duk wani dan ta’addar da aka san mafakar sa.
Ya ce saka CJTF na da muhimmanci a wannan shiri, domin sun fi sanar sirrin kowane daji, sako da kuma sanin fuskokin wasu ‘yan Boko Haram din da dama.
A wurin kaddamarwar dai an nuno Buratai da Gwamna Zulum rike da kyallen yadin fasta mai dauke da hotunan dukkan ‘yan ta’adda sama da 80 din da ake farauta.
Janar Buratai ya kuma jaddada wa sojoji cewa wannan farauta ita ce tamkar matakin karshe na fatattakar Boko Haram dungurugum. Don haka kada su sassauta wa wani dan Boko Haram.
Ya bayanna muhimmancin saka ‘yan CJTF cikin rundunar farautar, inda ya ce sun di sojoji sanin surkukin dazuka kuma sun san wasu ‘yan Boko Haram din.
“CJTF sun dade su na taka muhimmiyar rawa a wurin yaki. Tun a karni na 18 sojoji ke amfani da CJTF lokacin yake-yake a kasashen Turai.” Inji Buratai.
Gwamna Zulum ya jaddada ci gaba da bayar da gudummawar ganin an yi nasarar dakile Boko Haram. Har ma ya bada gudummawar babura 100 domin sojoji su rika amfani da su wajen shiga surkukin dazukan da ke wa motoci wahalar kutsawa.
Shi ma Babban Kwamandan Operation Lafiya dole Farouq Yisuf, ya jinjina wa CJTF kuma ya karfafa masu guiwa.