Shugaban INEC, Yakubu Mahmood ya mika ragamar shugabanci ga mai rikon kwarya

0

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya miƙa ragamar mulkin hukumar ga Kwamishinan Kasa a hukumar, Air Vice Marshal (AVM) Ahmed Mu’azu (ritaya) kafin ya samu amincewar ci gaba da mulkin sa a karo na biyu.

A wani kwarya-kwaryan taron mika ragamar wanda aka yi a hedikwatar INEC a Abuja a ranar Litinin, Farfesa Yakubu ya bayyana cewa bai dace a gare shi ya ci gaba da aiki ba daga ranar 9 ga watan Nuwamba, domin a ranar ne wa’adin sa ya kare, ba tare da Majalisar Dattawa ta tabbatar masa da wa’adin sa na biyu ba.

An rantsar da Yakubu da Kwamishinoni biyar ne a ranar 9 ga Nuwamba, 2015, sannan aka rantsar da wasu Kwamishinoni shida a ranar 7 ga Disamba, 2016, da kuma karin Kwamishina daya a ranar 21 ga Yuli, 2018.
 
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa har yanzu Yakubu ya na jiran Majalisar Dattawa ta amince da sabon nadin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi masa a ranar 27 ga Oktoba, a karo na biyu.

Yakubu ya ce Tsarin Mulki ne ya kafa hukumar kuma an naɗa membobin ta ne bisa wa’adin shekara biyar wanda za a iya sabuntawa a karo na biyu na karshe.

Ya ce: “Wannan na nufin cewa wa’adi na da na Kwamishinoni biyar na farko da aka nada ta kare a yau.
 
“Kamar yadda ku ka sani, an riga an bayyana sabunta nadi na a matsayin Shugaban Hukumar, bisa amincewar Majalisar Dattawa.

“Aikin mu a matsayin manajojin gudanar da zabe ya na bukatar mu bi doka da ka’idoji.

“A wajen yin hakan, tilas ne mu nuna tsantar girmamawa ga tare da kiyaye Tsarin Mulki da dokokin Nijeriya.
 
“Sakamakon haka, ba zai dace ba a gare ni in ci gaba da gudanar da aiki bayan yau din nan, 9 ga Nuwamba, ba tare da amincewar Majalisar Dattawa da kuma sake rantsar da ni ba kamar yadda doka ta tanada.

“Kafin zuwa lokacin da za a kammala bin wannan tsarin na doka, sauran Kwamishinonin Kasa sun yanke shawarar cewa AVM Ahmed Mu’azu (ritaya) zai rike ragamar hukumar.
 
“Saboda haka, ina mai farin cikin mika ragamar a gare shi a wannan lokaci. Mun yi aiki tare a matsayin guruf ɗaya a tsawon shekaru hudu da su ka gabata. Don haka, babu wani sabon abu ga kowannen su.”

Yakubu ya yi godiya ga membobin hukumar da kwamishinonin zabe na jihohi da sakataren hukumar saboda kyakkyawar huldar aiki da ya wanzu a tsakanin su.
 
Haka kuma ya gode wa darakta-janar na Makarantar Harkokin Zabe (Electoral Institute) da daraktoci, membobin sashen aiwatarwa, shugabannin hukumomin tsaro daban-daban da aka tura su zuwa INEC da dukkan ma’aikatan hukumar da ke dukkan fadin kasar nan. Ya ce, “Ina sa ran ci gaba da aiki tare da ku.”

Shi dai AVM Mu’azu, wanda shi ne kwamishinan kasa mai kula da Hukumar Karbar Bayanan Kwangila a INEC, ya yi alƙawarin rike ragamar hukumar bakin iyawar sa har zuwa lokacin da majalisa za ta amince da nadin Yakubu ya dawo bakin aiki a wa’adin sa na biyu.

Mu’azu ya ce nauyin da aka dora masa ba sabon abu ba ne a gare shi saboda dukkan kwamishinonin na kasa a lokuta daban-daban sun yi shugabancin riƙon kwarya na INEC, a duk lokacin da ya tafi aiki a ƙasar waje.

Ya ce, “A tsawon shekaru hudu da su ka gabata, ya kasance al’adar shugaban cewa a duk lokacin da zai tafi wata ƙasa ya kan ba wani kwamishinan kasa riƙon ƙwaryar shugabancin hukumar.

“Ta haka ne dukkan kwamishinonin kasa su ka riki mukamin muƙaddashin shugaba. Don haka, a haka ne mu ke kallon tsarin da aka yi a yanzu, ba wani abu daban ba.

“Ina so in tabbatar maku da cewa zan rike al’amuran hukumar nan bakin iyawa ta.”

Shi ma a nasa jawabin, wani kwamishinan kasa wanda wa’adin sa ya kare tare da na shugaban, Mista Solomon Soyebi, ya yaba wa nasarorin da Yakubu ya samu a wa’adin sa na farko.

Soyebi ya yi kira a gare shi da ya ci gaba da ayyukan da ya saba yi idan ya dawo bakin aiki a wa’adin sa na biyu.

Share.

game da Author