Kungiyar Ƴan Kudancin Kaduna SOKAPU, ta yi kakkausar suka ga tsarin shirin samar da zaman lafiya da gwamnatin Kaduna take yi a musamman yankin kudancin Kaduna tsakanin mazauna ƴankin.
Shugaban ƙungiyar Jonathan Asake, ya soki duk wani shiri da tsari da gwamnati take yi don ganin an samu zaman lafiya a yankin cewa ‘ Tsaka Tsami’ ne domin ba a tafiya da wadanda suka cancanta a yi tafiyar da su ba.
” Wannan abu da gwamnatin El-Rufai ta ke yi abu ne wanda ba zamu amince da ita ba, domin an zabi wasu manya ne kawai ake tattaunawa da su maimakon a bi diddigi sannan a ji ra’ayin kowa da kowa, kuma muma a tuntube mu.
” Kiri-kiri Fulani za su far wa mutanen mu a kudancin Kaduna, amma gwamna El-Rufai zai fito karara ya ce wai rikicin kabilanci ne saboda son rai. Dole sai an bi wa ƴan uwan mu da Fulani suka zalinta hakki kafin mu yarda da wani zama wai na samar da zaman lafiya.
” Kawai an zabi wasu manya an hada kai dasu wai ana tsara yadda za a samu zaman lafiya a yankin Kudancin Kaduna.
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tunasar da Asake hare-haren da ka kai wa matsugunin Fulani makiyaya a yankunan garuwawan Kudancin Kaduna, ya ce Ƴan yankin Kudancin Kaduna, Kiristoci wadanda ba Hausa-Fulani ba, basu kai wa wani hari ba sai da aka tsakale su.
A karshe Asake ya ce kungiyar sa a shirye ta ke ta hada hannu da gwamnati don kawo karshen rashin zaman lafiya a yankin Kudancin Kaduna.
Game da zargin da ake yi wa gwamnatin El-Rufai kan nuna son kai da ɓangaranci, kakakin gwamnatin jihar, Muyiwa Adekeye ya ce gwamnan Kaduna ba mutum mai irin wadannan halayya, ” Ku duba ko a jihar Kaduna, hatta wadanda ba ‘yan asalin jihar ba duk ya basu mukamai saboda shi ba ɗan ɓangaranci bane.