Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya ku jama’ah, sai mu kara yin godiya ga Allah Ta’ala, da ya kaddari masoyinmu, Ahmad Nuhu Bamalli shine ya zama Sarkin Zazzau na 19. Ina rokon Allah Ta’ala ya taya shi riko, ya dafa masa, kuma yasa masa hannu cikin wannan nauyi da jagoranci da ya dora masa, kuma ya kare shi, ya tsare shi daga jin kunyar duniya da ta lahira, ya kare shi daga dukkan makircin masu makirci, amin.
‘Yan uwa na masu daraja, ya kamata mu san wanene wannan sabon Sarki na Zazzau. Domin mu kara hakikancewa akan cewa lallai a yau Zaria da al’ummarta sun dace, kuma sun yi sa’ar nagartaccen Sarki, mai ilimi, kuma mai kaunar jama’arsa.
To shi dai Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli shine Sarki na 19 a jerin sarakunan masarautar Zazzau, kuma shine Sarki na farko daga gidan Mallawa da ya hau gadon Sarauta cikin shekaru 100, bayan rasuwar kakansa Sarki Malam Aliyu Dan Sidi a shekarar 1920.
Kuma Ahmad Nuhu Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa, sannan shine Magajin Garin Zazzau kafin naɗinsa Sarki a ranar Laraba, 7/10/2020.
Kuma Ambasada Ahmad ɗa ne ga Alhaji Nuhu Bamalli tsohon Magajin Garin Zazzau, kuma tsohon minista a Najeriya.
Kuma sabon Sarkin na Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli masanin shari’a ne da diflomasiyyah, shine jakadan Najeriya a Thailand kafin ya zamo Sarki.
Saboda girman sarautarsa ta Magajin Garin Zazzau, da kirkinsa, da mutuncinsa, da haba-habarsa da jama’ah, da kuma kusancinsa da gwamnati yasa aka rinka sanya shi a jerin waɗanda ka iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.
An haifi Ahmad Nuhu Bamalli a birnin Zaria, ranar 8 ga watan Yuni na 1966.
Mahaifinsa, Alhaji Nuhu Bamalli, yana cikin mutanen da suka yi fafutukar samun ‘yancin kan Najeriya, kuma ya taba zama ministan harkokin wajen kasar, sannan ya rike sarautar Magajin Garin Zazzau, wadda dan nasa Alhaji Ahmad ya gada bayan rasuwarsa a 2001 (Ina rokon Allah ya gafarta masa, amin).
Sabon Sarkin na Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, yayi karatunsa na firamare da sakandare a garin Kaduna, sannan ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, inda yayi Digirinsa na farko a fannin aikin lauya a 1989.
Kazalika yayi Digirinsa na biyu (Masters) a fannin harkokin kasashen duniya da diflomasiyya a Jami’ar ta Ahmadu Bello a 2002.
Sannan Jami’o’in da ya halarta domin yin wasu kwasa-kwasai sun haɗa da Harvard da Oxford da Northwestern University da ke Chicago da kuma Jami’ar Pennsylvania da ke Amurka.
Ahmad Nuhu Bamalli yayi kusan ɗaukacin rayuwarsa ta aiki ne yana aiki a bankuna, inda kuma ya taɓa yin aiki a kamfanin da ke buga kudin Najeriya (Nigerian Security Printing and Minting).
A shekarar 2017 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin jakadan kasar a Thailand. Gabanin nan, ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Hukumar Zaɓe ta jihar Kaduna.
Sabon Sarkin na Zazzau yana da mata ɗaya, Mairo A. Bamalli da kuma ‘ya’ya biyar – namiji ɗaya da mata huɗu (Ina rokon Allah ya raya su, yasa masu albarka, amin).
• Muhimman abubuwan da ya kamata mu sani game da sabon Sarki a takaice:
1. An haifi Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a shekarar 1966 a birnin Zaria, Najeriya.
2. Yayi karatun aikin lauya a digirinsa na farko daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, a shekarar 1989. Digiri na biyu (masters) a harkokin kasashen waje da diplomasiyyah a dai duk jami’ar, shekarar 2002.
3. Kuma ya samu shaidar karatu ta Post Graduate Diploma akan gudanarwa, daga jami’ar kimiya da fasaha ta jihar Enugu, a shekarar 1988.
4. Yayi wani kwas akan sasanta rikice-rikice a jami’ar York da ke kasar Ingila, a 2009, kafin daga bisani ya wuce jami’ar Oxford da ke kasar Ingilar, in da ya samu takardar shaidar karatu ta Diploma a fannin jagoranci (organisational leadership), a shekarar 2015.
5. Sabon Sarkin na Zazzau, wato Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, babban kwararre ne, wato Senior Fellow, wanda yake da kwarewa ta shekaru ashirin da shida a harkar banki, hulda da jama’ah, harkar sadarwa da kuma sarrafa kayayyaki.
6. Kuma shi tsohon dalibin shahararriyar makarantar nan ce ta koyon harkokin kasuwanci (Harvard Business School), a inda ya samu shaidar takardar karatu ta GMP, a 2011.
7. Sannan mukamin da ya rike kafin zamansa Sarkin Zazzau, wato Magajin Garin Zazzau, shine babban mukami na biyu a duk fadin masarautar Zazzau.
8. Yana zaune lafiya da iyalinsa, kuma cikin koshin lafiya. Yana auren Hajiya Mairo A. Bamalli, kuma suna da ‘ya ‘ya biyar, namiji daya mata hudu. Ina rokon Allah Ta’ala ya albarkace su, amin.
9. Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, kafin hawansa sarautar Zazzau mai daraja, shine ambasadan Najeriya a kasar Thailand, da kuma Republic of the Union of Myanmar.
10. Ya rike mukamin Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kan ta na jihar Kaduna, tsakanin 2015 zuwa 2017.
11. Sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya taba rike mukamin Acting Managing Director/Chief Executive Officer and ED Corporate Services a Nigeria Security Printing and Minting Plc, tsakanin 2011 zuwa 2014.
12. Tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009, ya taba rike mukamin Human Resources Manager a hukumar Nigerian Mobile Telecommunications Limited (MTEL).
13. Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya taba rike mukamin Chairman, Board of Directors, na Tawada Limited, wanda wani yanki ne na Nigeria Security Printing and Minting plc, daga shekarar 2012 zuwa 2014.
14. Kuma shi member ne na Transition Committee na jihar Kaduna, a shekarar 2016.
15. Kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya taba zama ma’aikaci a hukumar Abuja Metropolitan Management Agency.
16. Sannan uwa-uba, sabon Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, duniya ta shaida cewa, shi mutum ne mai gaskiya, mai rikon amana, mai hakuri, mai nuna jaruntaka da kwazo, da juriya, da jajircewa a cikin dukkanin al’amurransa; sannan shi mutum ne mai kishin addininsa, mai taimakon addini, mai taimakon al’ummah, mai tausayi, mai son talakawa, mai kaunar zaman lafiya, hadin kai da ci gaba; Shi mutum ne marar nuna banbanci ko kabilanci, shi mai kaunar jama’ah ne matuka, kuma mai kyauta, mai alkhairi. Sandiyyar haka nike shaidawa ‘yan uwana Zazzagawa, da dukkanin mutanen arewa, da ma Najeriya baki daya cewa, su sani, da yardar Allah, Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ba zai taba basu kunya ba! Da yardar Allah, sai an ji dadi, kuma sai an yi murna da zamansa Sarkin Zazzau. Sai ance gwamma da aka yi da yardar Allah, Mahaliccinmu.
Sannan ina kira, da roko, da lallashi ga dukkanin al’ummah, cewa, lallai ya zama wajibi, ya zama tilas, ya zama dole muci gaba da yiwa wannan bawan Allah, wato Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, da sauran shugabannin mu, addu’a da rokon Allah yasa su gama lafiya, Allah ya kama hannayensu, yayi riko da hannayensu, ya dora su akan abun da yake daidai, wanda Allah yake so, kuma ya yarda da shi, amin thummah amin.
Daga karshe, muna nan muna ta addu’o’i da rokon Allah Ta’ala ya taya shi riko, amin. Da yardar Allah ba zamu gajiya ba akan wannan!
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a lambar waya kamar haka: 08038289761.