SHIGA JAMI’A: Alfarmar ƙanƙantar maki a jarabawar UTME ta maida matasan Arewa ragwaye – El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa alfarmar da gwamnati ke wa matasan Arewa wajen yanka masu tsaka-tsakiyar makin shiga jami’a a jarabawar UMTE ta maida matasan Arewa ragwaye wajen tashi tsaye su yi karatu sosai.

Ya ce matasan na Arewa sun yi kwance turus, sun kasa amfani da damar da aka ba su, wadda ‘yan sauran yankunan kasar nan ba su samu ba, wajen mikewa tsaye inganta damar samun ilmi nagartacce.

El-Rufai ya yi wannan tsinkaye ne ranar Talata a wajen ba taron Makomar Tattalin Arzikin Najeriya.

“Matasan Arewa sun samu dama, amma sun kasa aiki da ita. Sun kasa cin moriyar ta. Su na samun damar shiga jami’a a karkashin makin da Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a, JAMB ke ba su, ba tare da cin maki mai tarin yawa ba. Amma saboda ragwanci da lalaci sun kasa amfani da wannan damar.

“JAMB ta ce ta na bada bambancin ka’idar yawan makin shiga jami’a ga jihohi daban-daban. Kuma wai haka gina kasa ake yi. Ana gina kasa ko dai ana rusa ta?”

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dandanzon milyoyin kananan yara masu gararamba kan titinan Arewa, babbar bazarana ce matuka.

“Ni dan Arewa ne, mun zama komabaya a fannin ilmi. Sannan JAMB na ba mu karancin adadin makin shiga jami’a, wai don mu tarad da sauran yankunan da su ka yi mana rata. Shin mun taras da su din?”

“Wannan alfarma da aka yi wa matasan Arewa na kara susuntar da su, su na kara zama ragwaye, koma-baya a fagen ilmi.” Inji El-Rufai.

Ba Tsarin Karba-karba Ne Maganin Matsalar Tattalin Arzikin Najeriya Ba:

PREMIUM TIMES ta buga labarin da El-Rufai ya ce karba-karba ba zai magance matsalar tattalin arzikin Najeriya ba.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa tsarin karba-karba ba shi ne zai iya magance tulin matsalar tattalin arzikin Najeriya ba.

Gwamnan ya yi wannan bayani a jawabin sa wurin Taron Makamar Tattalin Arziki na Kasa, inda ya ce karba-karba ba hanya ce ta tabbacin magance tattalin arziki ba.

Duk da tsarin karba-karba ba ya cikin tsarin mulki, amma jam’iyyu da ‘yan siyasar Najeriya na yin tsarin karba-karba tsakanin Arewaci da Kudancin Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari da ke kai a zango na biyu, ana sa ran bayan ya kammala, mulki zai koma a hannun kudancin kasar nan.

Cikin watannin nan batun maida mulki a hannun ‘yan kudu ya rika tayar da hayaki, har ta kai gwamnan jihar Ebonyi, David Omahi, ya fice daga PDP ya koma APC.

Umahi ya yi zargin cewa ya fice daga PDP, zuwa APC, saboda ya gano cewa PDP ba za ta bada takarar shugaban kasa a hannun dan yankin Kudu maso Gabas, wato yankin jihohin kabilar Igbo.

Shi ma Ministan Ayyukan Babatunde Fashola, wasu jaridu sun ruwaito shi ya na cewa a 2023 ya kamata mulki ya koma kudu.

Amma shi kuwa El-Rufai, cewa ya yi karba-karba ba zai fitar da Najeriya daga matsalar tattalin arziki ba. Don haka ya ce kamata ya yi a ba kowa ‘yanci da damar fitowa takara, sai a tantance a dauki guda daya kwakkwara mai nagarta.

Ko cikin watan Agusta sai da El-Rufai ya ce kamata ya yi a yi watsi da karba-karba, a bi cancanta kawai. Ya ce ko ma daga ina wanda ya fi cancanta ya ke, to sai a ba shi takara kawai.

Cikin Agusta kuma gwamnan na Kaduna ya ce bai kwamata ‘yan Arewa su tsaya takarar zaben shugaban kasa ba.

Cikin Oktoba 2019, PREMIUM TIMES ta buga labarin da tsohuwar babbar jami’ar diflomasiyya ‘yar Amurka, Linda Greenfield, ta ce siyasar Najeriya za ta samu kanta cikin yanayi mai tsauri idan zaben shugaban kasa na 2023 ya zo.

Share.

game da Author