Najeriya ta sake ruftawa cikin kunci da matsin tattalin arzikin da shekaru 40 ba ta shiga ba.
A karo na biyu tun bayan 2016, Najeriya ta sake afkawa cikin tabarbarewar tattalin arziki, yayin da ake shirin afkawa ramin da shekaru arba’in ba a shiga kunci irin sa ba.
A karo na biyu kenan, tattalin arzikin na Najeriya ya sake tabarbarewa, bayan ya tabarbare shekaru biyar da su ka gabata. Watanni shida kenan Malejin Bunkasar Tattalin Arzikin Cikin Kasa (GDP) ya yi tsaye cancak, ya kasa gaba. A gefe daya kuma sai tiriliyoyin bashi gwamnatin Buhari ke ta kara labtawa kan gadon bayan tabarbararren tattalin arzikin.
Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), wadda hukuma ce ta gwamnatin tarayya, ta bayyana wannan labari maras dadin ji.
NBS ta ce tsawon watanni shida kenan tattalin arzikin Najeriya ya kasa motsawa gaba. Har yau a kashi 3.62 ya ke, ga shi an shiga wasu wasu watanni uku masu hatsari, ga shi kuma 2020 ta na gab da karewa, sannan kuma za a shiga shekarar 2021 za a shiga, shekarar likimon bashi a wuyan Najeriya.
Baya ga bashin da Najeriya ke kara labtawa kan ta, kusan rabin kudin da Najeriya ke samu a duk wata, ya na tafiya ne wajen biyan basussuka da kuma biyan kudin ruwan basussukan da ba a kai ga fara biya ba.
Yadda Mai Karatu Zai Iya Gane Ko Karayar Arzikin Najeriya Ya Shafe Shi:
Karayar tattalin arziki na afkawa kan kasa idan tattalin arzikin ta ya ci gaba da dulmiyawa kasa maimakon ya yi sama, har tsawon watanni shida a jere.
To idan aka kai ga wannan mataki, ko kuma aka zarce a haka tattalin arziki ya tashi daga karyewa, ya kai ga tabarbarewa.
Ana auna karfin tattalin arzikin kasa da karfin nauyin awon sikelin GDP na kasar. Shi kuwa GDP, shi ne karfin darajar abin da kasa ke samarwa ko ta ke kerawa ko kirkira a cikin kasar, ba tare da ta dogara da na kasar waje ba, har tsawon shekara guda.
Zuwa karshen Satumba sai karfin tattalin arzikin cikin gida na Najeriya (GDP), ya kai darajar naira tiriliyan 39, kuma shi ne mafi karfi a dukkan kasashen Afrika.
Idan tattalin arziki ya bunkasa, to al’ummar kasa kan kara samun karuwar arziki, a samu karin arrajirai, a samu aikin yi, akbashin ma’aikata ya karu, rayuwa ta inganta, kuma a samu yalwar arziki.
Sannan kuma masu zuba jari a masana’antu, cibiyoyin hada-hada da harkokin kasuwanci su kara samun riba.
Gwamnati na karuwa idan tattalin arziki ya bunkasa, ta hanyar karin samun kudin shiga na haraji daban-daban. A gefe daya kuma zai kasance gwamnati na da tulin kudi ajiye dankam, wadanda za ta rika kaahewa wajen gudanar da ayyukan inganta al’umma da raya kasa, ba tare da wata jikarar sai ta jira ta ciwo bashi ba.
Yadda Kasa Ke Ruftawa Kogon Ramin Karayar Tattalin Arziki:
Idan aka samu kasa na ci baya har tsawon watanni uku sau biyu kuwa, wato watanni shida a jere, to kafafun sa biyun da ya ke tsaye da su sun yi sanyi kenan. Ba su da nauyin daukar lodin matsalolin da su ka dabaibaye tattalin arzikin kasar.
Wannan kuwa gagarimar matsala ce ga kowace kasa duk karfin ta a duniya.
Rabon da Najeriya ta samu kan ta a wannan yanayi tun cikin 2015/2016.
Manyan Dalilai:
Manyan dalilai dai ba su wuce yawan bashin da ya kumbura wa Najeriya ciki, har numfashi mai karfi ke neman gagarar tattalin arzikin kasar. Akwai kuma karancin kudi a aljihun gwamnatin tarayya.
Masana sun amince cewa halin da Najeriya ta fada a wannan lokacin ya wuce irin wanda kasar ta rufta a baya, musamman saboda dukan-kabarin-kishiya da matsalar cutar korona ya yi wa tattalin arzikin ta.
Yadda Karayar Tattalin Arzikin Najeriya Ke Shafar Talaka:
1. Karancin kudi, ta yadda za ka kasa warware wa kan ka matsalar da ka ke iya warware wa a baya.
2. Yawaitar rasa aiki da yawan kora ko sallamar ma’aikata.
3. Za a ga masana’antu da kamfanoni na rage yawan albashin ma’aikatan da ba a kora ba.
4. Karancin kudin shiga ga gwamnati, ta yadda za ta kasa gudanar da wasu ayyuka. Ko dai sai ta ciwo bashi, ko kuma a hakura.
5. A kasa gudanar da wasu muhimman ayyukan inganta kiwon lafiya saboda karancin kudi.
6. Matsalar kan bijiro da yunwa da fatara da talaucin da ke nesa su shigo kane-kane cikin al’umma.
Ana magance wannan matsala ta hanyar rage kudin ruwa da Babban Bankin Najeriya zai iya yi, saisaita kudaden musaya na kasashen waje da naira da sauran su.